Wata Mata mai juna biyu tare da yayanta 2 sun gamu da ajalinsu a sanadiyyar gobara

Wata Mata mai juna biyu tare da yayanta 2 sun gamu da ajalinsu a sanadiyyar gobara

Mutuwa dayace, amma hanyoyinta da yawa, kamar yadda masu iya magana kan fada, anan kuma wata matace mai dauke da juna biyu ta yi asarar rayuwarta, tare da na yayanta guda biyu a sanadiyyar wata gobara da ta rutsa dasu.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan mummunan lamari ya faru ne a da misalin karfe 11 na daren Asabar, 9 ga watan Feburairu a gidansu dake unguwar Biri cikin garin Minna na jahar Neja, sakamakon wutan lantarki mai karfi da kamfanin wutar AEDC ta kawo.

KU KARANTA: Tura ta kai bango: Jama’an gari sun halaka yan bindiga guda 5 a jahar Katsina

Wata Mata mai juna biyu tare da yayanta 2 sun gamu da ajalinsu a sanadiyyar gobara

Adama, Taslim da Taslima
Source: Facebook

Mazauna unguwar sun bayyana cewa da misalin karfe 10 na daren Asabar aka dauke musu wuta, amma aka dawo dashi da bayan kimanin awa daya, daga nan sai aka fara samun tartsatsin wuta, wanda hakan ya janyo tashin gobarar.

Da yake cikin dare aka dawo da wutar, Matar da yayanta sun yi baci tuni, don haka ko kafin su farka hayaki ya turnuke dakunansu gaba daya, kamar yadda kanin mijin matar, Danjuma Mustapha ya bayyana, wanda yace yana kwance ya jiyo ihunta.

“A guje na garzaya dakinta wanda ya riga ya turnuke da hayaki, mun yi kokarin bude kofar dakinnata, amma duk kokarinmu bai bude wannan kofar ba, sakamakon wutar ta fara ci ganga ganga.” Inji shi.

Haka zalika duk da cewa jami’an hukumar kashe gobara sun isa unguwar da wuri, kuma sun tafi da manyan motocin kashe wuta har guda hudu, amma basu samu daman kutsawa zuwa gidan da wuri ba sakamakon rashin tsarin unguwar ta yadda kowa na gin gidansa ne yadda yaga dama.

“A lokacin da suka samu isa gidan da kyar,sai dai gawar Matar da na yayanta biyu kawai aka tarar, sun kone fiye fa misali.” Inji wani makwabcinsu, Malam Abubakar Muhammad.

Shima Maigidan matar, Usman Mustapha ya bayyana sunan mamatan kamar haka, Matarsa sunanta Adama Usman mai shekaru 28, Taslim mai shekaru 5 sai kuma Taslima mai shekaru 7, amma fa ya shiga cikin damuwa matuka, Allah Ya jikansu da gafara.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel