Buhari yana cigaba da fadawa Jama’a su zabi duk wanda su ke so

Buhari yana cigaba da fadawa Jama’a su zabi duk wanda su ke so

- Shugaban kasa Buhari yana cigaba da fadawa mutane su zabi kowa su ke so

- Buhari ya nemi al’umma su fito su dangwalawa duk wanda su ka ga dama

- Shugaban kasar yayi irin wannan da ya je Jihohin Imo, Ogun da ma Zamfara

Buhari yana cigaba da fadawa Jama’a su zabi duk wanda su ke so

Shugaban Kasa yayi kira ga jama’a su zabi kowa su ke so a 2019
Source: Twitter

Yayin da ake sa ran zaben Najeriya a karshen makon nan, mun samu labari cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari yana cigaba da kira ga mutanen kasar nan su zabi kowa su ka ga dama a babban zaben da za ayi.

A karshen makon nan ne shugaba Buhari yayi kamfe a Garin Zamfara inda ya fadawa mutanen jihar su fito su zabi duk wanda su ke so. Shugaban kasar dai bai nuna cewa dole sai an zabi ‘yan takarar jam’iyyar APC.

KU KARANTA: Jami'an tsaro sun hana ayi wa Buhari a-ture a Ogun

Ko a karshen jawabin shugaban kasar, ba a ji yana kururuwar APC SAK kamar yadda ya saba ba. Ya fadawa mutane su zabi duk wanda su ka ga dama. Kwanakin baya mai dai irin abin da shugaban kasar ya fada kenan a Imo.

A jiya ne kuma jirgin yakin shugaba Buhari ya isa jihar Ogun inda ake rikici tsakanin Dapo Abiodun wanda yake tare da APC da tsohon gwamna Segun Osoba da kuma Adekunle Akinlade wanda Gwamna mai-ci yake so.

Shugaban kasar ya fadawa mutanen jihar ta Ogun su zabi duk ‘dan takarar da ya kwanta masu a rai a zaben gwamnan da za ayi a Ranar 2 ga Watan Maris. APC ta dai mikawa Dapo Abiodun tuta wanda ya sa aka fara rikici.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel