Dalilin da yasa al'ummar Adamawa za su zabi Buhari - Talban Adamawa

Dalilin da yasa al'ummar Adamawa za su zabi Buhari - Talban Adamawa

Talban Adamawa, Daniel Bwala ya ce idan ba domin matakan da Shugaba Muhammadu Buhari ya dauka na samar da tsaro a yankin Arewa maso Gabas ba, da yanzu ba za a samu wani mahaluki mai rai a jihar ta Adamawa ba.

Ya ce saboda wannan kadai, al'ummar jihar Adamawa za su goyi bayan Shugaban kasa da jam'iyyarsa ta All Progressives Congress (APC) a babban zaben da ke tafe a ranar Asabar.

A hirar da Bwala ya yi da Punch a ranar Litinin, ya ce al'ummar jihar ba za su taba mantawa da halin rashin tsaro da jihar ta fada ba kafin zuwan Shugaba Muhammadu Buhari.

Ya yi ikirarin cewa wasu al'ummar jihar ba su taba dandana romon demokradiya ba har sai lokacin da gwamnatin APC da shugaba Muhammadu Buhari suka dare a kan mulkin kasar nan.

DUBA WANNAN: Jiga-jigan 'yan siyasar Najeriya da ba su taba sauya sheka ba

Dalilin da yasa al'ummar Adawama za su zabi Buhari - Talban Adamawa

Dalilin da yasa al'ummar Adawama za su zabi Buhari - Talban Adamawa
Source: UGC

Ya ce duk da cewa dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, Atiku Abubakar dan jihar Adamawa ne, duk da haka mutanen jihar Buhari za su zaba.

Bwala ya ce, "A jihar Adamawa, zai yi wahala mu manta cewa ba domin zuwan shugaba Muhammadu Buhari ba, da da yawan mu munyi hijira daga jihar nan mun koma wasu jihohi.

"Mun rasa 'yan uwa da abokan arziki saboda rikicin kungiyar Boko Haram a baya. Adadin mu ya ragu sosai domin ana ta kashe mana yaran mu da mazajen mu.

"'Yan ta'ada na amfani da yaran mu mata domin kunar bakin wake. Mummunan abinda muke tunawa kenan idan munyi waiwaye a baya.

"Amma yanzu abubuwa sunyi sauki. Manoma suna zuwa gona ba kaman a baya ba da 'yan ta'ada suka kwace gonakin mu.

"Mun ga irin kokarin da shugaban kasa ya yi kuma hanya daya da zamu nuna godiyar mu shine mu kara zabensa na shekaru hudu domin ya karasa ayyukan da ya fara.

"Duk da cewa akwai dan garin mu da ke takarar shugabancin kasa shima, Buhari za mu zama saboda mun gwada shi kuma mun gamsu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel