Malamai su daina tsunduma kan-su cikin fagen siyasa – Kwankwaso

Malamai su daina tsunduma kan-su cikin fagen siyasa – Kwankwaso

- Rabiu Musa Kwankwaso yayi kira ga Malamai su guji shiga cikin harkar siyasa

- Sanatan na Kano ta tsakiya ya nemi a maka sa a Kotu game da wasu kwangiloli

- Tsohon Gwamnan ya kuma ce PDP ce za ta ci zabe a Kano duk da ba su da mulki

Malamai su daina tsunduma kan-su cikin fagen siyasa – Kwankwaso

Kwankwaso yace idan an isa a fito da bidiyon sa yana karbar Daloli
Source: Twitter

Mun samu labari cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya sake yin kira ga Malaman addini da su daina sakin layi su na shiga cikin lamarin siyasa. A baya Sanatan na Kano yayi irin wannan kashedi ga Malaman.

Rabiu Kwankwaso yayi wannan bayani ne lokacin da aka yi hira da shi a gidan rediyon Express FM na Kano inda yace bai kamata Malamai masu karantar da jama’a su rika sukar ‘yan takaran da ke PDP ba muddin cewa ba za su yabe su ba.

KU KARANTA: Buhari zai fadi zabe - Inji PDP bayan ta ga taron Jama'a a Kano

Tsohon gwamnan yake cewa akwai Malamai wadanda da aka sani da mutunci har ya kama sunayen wasu daga cikin manyan Shehunnan Kano da ya kira da Magada Annabawa inda ya kuma ce akwai bata-gari wanda su ke Magada Daloli.

Injiniya Kwankwaso ya bayyana cewa ba su neman tada fitina a jihar ya kuma gargadi duk masu kokarin jawo rikici a zaben da za ayi. Sanatan yace yana da tabbacin cewa PDP za tayi nasara a zaben da za ayi duk ba su da gwamnati a hannu.

Sanatan ya kuma kalubalanci gwamnatin jihar Kano ta bankado zargin da ake yi na cewa tsohuwar gwamnatin sa ta lakume kudin yin hanyoyi a kananan hukumomin jihar inda ya kuma yi tir da zargin da ke wuyan Ganduje na karbar rashawa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel