Kudin makamai: An yi gum da zargin Ministan Buhari da kuma NSA

Kudin makamai: An yi gum da zargin Ministan Buhari da kuma NSA

- A 2016 ne aka soma bincike game da badakalar kwangilolin makamai

- Akwai wasu mukarabban Buhari da aka nemi a bincika tun a lokacin

- Har yanzu dai babu wanda ya taba Janar Dambazau da kuma Munguno

Kudin makamai: An yi gum da zargin Ministan Buhari da kuma NSA

Babu labarin binciken Babagana Monguno da Abdulrahman Dambazau
Source: Depositphotos

Fiye da shekaru biyu kenan da aka nemi a binciki Mai ba shugaban kasa shawara kan harkar tsaro watau Manjo Janar Babagana Monguno; da kuma Ministan harkokin gida, Janar Abdulrahman Dambazau amma shiru har yanzu.

Wani kwamiti da aka nada domin yayi bincike game da harkar sayen makamai a Najeriya daga 2007 zuwa 2015, ya bada umarni a binciki manyan tsofaffin sojojin kasar irin su Janar Abdulrahman Dambazau da NSA B. Munguno.

KU KARANTA: Janar Buratai yayi sabon alwashi na kauda ‘Yan Boko Haram

Kwamitin ya nemi a tuhumi Laftana Janar Abdulrahman Dambazau mai ritaya ne saboda matsayin da ya rike da shugaban hafsun sojin kasa a 2008 zuwa 2010 yayin da shi kuma Babagana Monguno ya rike mukamin CDI a gidan Soja a 2011.

Tuni dai an damke da dama daga cikin wadanda ake tuhuma da laifi daga rahoto wannan kwamiti. Manyan sojoji irin su Kanal Sambo Dasuki tuni su ka shiga hannu amma kuma shi dai Manjo Janar Munguno da Ministan babu batun taba su.

A farkon 2016 ne gwamnati ta taso keyar manyan sojojin Najeriya kusan 300 domin a bincike su. Wadannan sojoji sun hada da wadanda su kayi ritaya da kuma masu aiki a yanzu. Babu wanda yace uffan ga wadanda ke kusa da gwamnati.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel