Zabe: AD, MAAN, NAC da NHRC sun goyi bayan Buhari

Zabe: AD, MAAN, NAC da NHRC sun goyi bayan Buhari

A ranar Litinin, 11 ga wata ne wasu kungiyoyi da jam’iyyun siyasa su ka fito fili su ka bayyana goyon bayan su ga takarar shugaba Buhari.

Jam’iyyar AD a jihar Oyo na daga cikin jam’iyyun da su ka bukaci magoya bayan su da su kada kuri’un su ga shugaba Buhari, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC.

AD ta bayyana hakan ne bayan kamala wani taro a sakatariyar jam’iyyar da ke garin Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Daga cikin jiga-jigan ‘ya’yan jam’iyyar da su ka halarci taron jam’iyyar ta yanke shawarar goyon Buhari akwai dan takarar ta na gwamna a jihar Oyo, Injiniya Hakeem Alao; tsohon mamba a majalisar wakilai, Tajuddeen Adeniji da shugaban jam’iyyar a jihar, Mista Adeola Adepoju.

Zabe: AD, MAAN, NAC da NHRC sun goyi bayan Buhari

Buhari
Source: UGC

Kazalika, kungiyar manoman masara ta kasa (MAAN) ta ce ta na goyon bayan takarar shugaba Buhari a zaben da za a yi ranar Asabar mai zuwa. MAAN ta dauki alkawarin samar wa da shugaba Buhari kuri’u miliyan biyar.

Shugaban kungiyar MAAN, Alhaji Bello Abubakar, ne ya bayyana haka yayin wani taro a Abuja, in da ya bayyana cewar adadin masarar da ake nomawa a Najeriya ya karu daga MT miliyan 15 zuwa MT miliyan 20 sakamakon kokarin gwamnatin Buhari a bangaren noma.

DUBA WANNAN: Fusatattun matasa sun tilasta tashin taron kamfen din Buhari a Ogun

Ita kuma jam’iyyar NAC, watsi ta yi da dan takarar ta, Ezeuko Emeka, tare rungumar shugaba Buhari a matsayin dan takarar da su ke goyon baya.

A na ta bangaren, kungiyar kare hakkin bil’adama ta Najeriya (NHRC) shawartar ‘yn Najeriya ta yi da su yi karatun ta natsu a kan alkawuran da jam’iyyar adawa ke yi don samun kuri’u a zaben ranar 16 ga watan Fabrairu. NHRC ta bukaci jama’a su yi waiwaye a kan shekaru 16 da jam’iyyar PDP ta yi a kan mulki tare da auna su bias mizanin irin nasarorin da gwamnatin APC ta samu a cikin sheakaru 4 kacal.

NHRC tare da ragowar wasu kungiyoyi 135 da su ka yi wani taro a Maryland da ke jihar Legas sun bayyana goyon bayan su ga takarar shugaba Buhari da mataimakin sa, Farfesa Yemi Osinbajo.

Sakataren NHRC, Taiwo Adeleye, ya ce ‘yan Najeriya za su yi zabe ne tsakanin jam’iyyar PDP da APC da kuma wasu ragowar jam’iyyu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel