An kama mutum 50 kan rikicin siyasa a Kano

An kama mutum 50 kan rikicin siyasa a Kano

Rundunar 'yan sanda ta jihar Kano a Najeriya ta ce ta yi nasarar kama mutane 50 da take zargi da bangar siyasa da kwace a yayin taron siyasa da aka gudanar na PDP a jihar ranar Lahadi.

A ranar Lahadi ne 'yan daba suka rika far wa mutane tare da yi masu kwace jim kadan bayan ziyarar da dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya kai jihar Kano domin yakin neman zabe.

An kama mutum 50 kan rikicin siyasa a Kano

An kama mutum 50 kan rikicin siyasa a Kano
Source: Twitter

KU KARANTA: Diyar Buba Galadima ta halarci taron kamfe din Buhari

Lamarin da ya jawo asarar rayuka da tare da ji wa mutane munanan raunuka.

Legit.ng Hausa ta tsinkayi kwamishinan 'yan sandan jihar ta Kano CP Muhammad Wakili yana cewa babu wanda ya fi karfin doka kuma duk ko waye kuma komai mukaminsa za su kama shi sannan su hukunta shi, don doka gaba take da kowa.

Har wa yau, ya kuma ce rundunar 'yan sandan jihar za ta sanya kafar wando daya da masu sayar da kwaya da kayan maye a jihar. Wakili Mohammed ya ja hankalin iyaye da su ja kunnen 'ya'yansu kan shiga bangar siyasa don guje wa fushin hukuma.

Yanayin siyasa a jihar Kano na kara munana duk da yarjejeniyar da yan takara suka sanya wa hannu kan yakin neman zabe da gudanar da zaben cikin lumana a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel