Kotu ta aika wa Oshiomhole sammaci kan rikicin APC a jihar Imo

Kotu ta aika wa Oshiomhole sammaci kan rikicin APC a jihar Imo

- Kotu ta aikawa da shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole sammaci kan sabawa umarnin ta

- Babbar kotun tarayya da ke garin Abuja ta nemi Oshiomole da ya gurfana gaban ta a mako mai zuwa

- Kotu ta aikawa Oshiomhole sammaci sakamakon sauke shugabannin APC reshen jihar Imo

Za ku ji cewa shugaban jam'iyyar APC na kasa, Kwamared Adams Oshiomhole, ya yi kacibus da sammacin babbar kotun tarayya da ke garin Abuja inda ta nemi ya gurfana gaban ta a mako mai zuwa kan dambarwa ta sauke shugabannin APC reshen jihar Imo.

Kamar yadda jaridar The Guardian ta ruwaito cewa, ana bukatar Oshiomhole ya bayar da shaidar dalilai da za su hana a tasa keyar sa zuwa gidan kaso bayan babban laifin da ya aikata na kunnen kashi da sabawa umarnin kotu.

Kotu ta aika wa Oshiomhole sammaci kan rikicin APC a jihar Imo

Kotu ta aika wa Oshiomhole sammaci kan rikicin APC a jihar Imo
Source: Depositphotos

Rahotanni sun bayyana cewa, a ranar 14 ga watan Agusta na shekarar 2018 da ta gabata, babbar kotun tarayya ta bayar da umarni ga Oshiomhole da kuma jam'iyyar sa ta APC akan haramci na sauke zababbun shugabannin jam'iyyar reshen jihar Imo bisa jagorancin Daniel Nwafor.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, bayan kunnen uwar shegu na sauke shugabannin jam'iyyar, Oshiomhole ya kuma yi nadin sabbin shugabannin ta tare da mika akalar jagoranci a hannun Marcellinus a matsayin jagoran jam'iyyar na jihar.

KARANTA KUMA: Cikin Hotuna: Al'umma sun yi tururuwa yayin yakin zaben Atiku a jihar Ribas

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, an yiwa jiga-jigan jam'iyyar APC ruwan duwatsu yayin taron yakin neman zaben kujerar shugaban kasa da shugaba Muhammadu Buhari ya gudanar cikin birnin Abeokuta na jihar Ogun.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel