Zalunci: An kama wasu ma’aikatan INEC da laifin karbar kudin ma su katin zabe

Zalunci: An kama wasu ma’aikatan INEC da laifin karbar kudin ma su katin zabe

Hukumar zabe mai zaman kan ta (INEC) ta sanar da cewar ta mika wasu ma’ikatan ta hannun jami’an tsaro bayan samun su da laifin karbar kudi daga hannun ma su son karbar katin zaben sun a dun-dun-dun.

Kwanishinan INEC a jihar Akwa Ibom, Mike Igini, ne ya sanar da hakan yayin wata hira ta wayar tarho da aka yi da shi a wani shirin gidan talabaijin na Channels mai taken “Sunrise Daily”.

Sai dai yanzu haka INEC ta canja wa Mista Ogini wurin aiki daga jihar Akwa Ibom zuwa Bayelsa.

Ma su son karbar katin zabe sun sha koka wa a kan wahakar da su ke fuskanta a kokarin sun a ganin sun karbi katin zaben su daga ofisoshin INEC.

Zalunci: An kama wasu ma’aikatan INEC da laifin karbar kudin ma su katin zabe

katin zabe
Source: Depositphotos

Mista Ogini ya tabbatar da cewar akwai jami’an INEC da aka samu da laifin karbar kudi daga hannun ma su son yin rijistar zabe da kuma ma su son karbar katin zaben su. Kazalila, ya bayyana cewar wasu daga cikin irin wadannan jami’ai da aka kama an mika su hannun jami’an tsaro domin daukan matakin da ya da ce a kan su.

DUBA WANNAN: Zabe: INEC ta warware kokonto ‘yan Najeriya a kan na’urar tantancewa

Ko a cikin makon jiya sai da Legit.ng ta kawo ma ku labarin cewar hukumar tsaro ta farin kaya a jihar Ribas ta gurfaar da wasu ma’aikatan hukumar zabe mai zaman kan ta (INEC) a gaban wata kotun majistare da ke Fatakwal bias zargin su da laifin sata tare da sayar da katin zabe (PVC) 3,097 da ke ofishin INEC.

An gurfanar da ma’aikatan na INEC da ke aiki a karamar hukumar Opobo Nkoro tare da wani dan siyasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel