Ritayar Kukasheka: Rundunar soji ta nada sabon kakaki, ta yi canje-canje

Ritayar Kukasheka: Rundunar soji ta nada sabon kakaki, ta yi canje-canje

Rundunar soji ta kasa ta saki sabbin canje-canjen wurin aiki da ta yi wa manyan jami’anta, kamar yadda ya ke a cikin sanarwar da Kanal Aliyu Yusuf ya fitar da safiyar yau, Litinin.

Wadanda canjin ya shafa sun hada da Birgediya Janar NJ Okah, wanda aka dauke daga makarantar fasaha da muhalli ta soji zuwa hedikwatar rundunar soji a matsayin darektan sashen kula da shige da fice; Birgediya janar HT Wesley, wanda aka nada a matsayin sabon darekta mai kula da tufafi da ma’ajiya a hedikwatar rundunar soji; da Birgediya MA Masanawa, wanda aka canja daga darekta a sashen fasaha da zuwa kwamanda na ACADA.

An canja Birgediya janar HG Tafida daga kula da dakin kere-kere na sojoji da ke Rigachikun zuwa sashen kula da shige da fice a hedikwatar rundunar soji.

Kazalika an mayar da Birgediya Janar BA Ilori zuwa sashen sayen kayan amfanin sojoji a hedikwatar rundunar soji.

Ritayar Kukasheka: Rundunar soji ta nada sabon kakaki, ta yi canje-canje

Manyan jami'an soji
Source: Depositphotos

An mayar da Kanal Onyeama Nwachukwu zuwa hedikwatar rundunar soji a matsayin mukaddashin darektan sashen labarai na rundunar soji.

DUBA WANNAN: Zabe: INEC ta warware kokonto ‘yan Najeriya a kan na’urar tantancewa

Kazalika an nada Kanal Sagir Musa a matsayin sabon mukaddashin kakakin rundunar soji, yayin da Kanal AA Yusuf zai kasance mataimakin sa

Ragowar da canje-canjen su ka shafa sun hada da kanal AD Isa; sabon mataimakin darekta a rundunar ofireshon lafiya dole da ke jihar Borno, Kanal S Adama; kwamandan likitocin soji, Kanal OG Olaniyi; mukaddashin darekta mai kula da sashen kade-kade, Kanal EI Okoro da Kanal IP Bindul; wadanda aka tura kwalejin horon yaki ta soji a matsayin ma’aikata da sauran su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel