Sabuwa: Yadda ake sayar da gyada akan titi ake sayar da 'kwaya' a Kano - Sabon Kwamishanan jihar Kano, Ali Wakili

Sabuwa: Yadda ake sayar da gyada akan titi ake sayar da 'kwaya' a Kano - Sabon Kwamishanan jihar Kano, Ali Wakili

Sabon kwamishanan jihar Kano, Muhammad Wakili, ya bayyana cewa muggan kwayoyi sun zama tamkar gyada a titunan jihar Kano yanzu, ya gargadi masu ta'amuni da wadanda kwayoyi ko kuma su fuskanci fushin hukuma.

Yayinda yake magana ke ranan Litinin jim kada bayan hawan sabuwar kujerarsa a Kano, Wakili ya bayyana cewa hukumar za tayi fito-na-fito da ta'amuni da muggan kwayoyi da zama ruwan dare a jihar Kano.

Saboda haka, Mista Wakili yayi kira da sarakunan gargajiyan jihar da shugabannin siyasa da su hada karfi da karfe wajn ganin cewa an kawo karshen wannan annoba da ya addabi jihar.

KU KARANTA: Da alamun Walter Onnoghen ya kusa taba kasa, NJC ta kara mika masa takardan zargi

Mun kawo muku rahoton cewa babban sufetan Yansanda, Mohammed Adamu ya tura shahararren jami’in Dansandan nan, Mohammed Wakili a matsayin sabon kwamishinan Yansandan jahar Kano kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Wakili yayi suna ne tun bayan bayyana wani faifan bidiyonsa a shafukan sadarwar zamani, inda yake magana akan yawaitar shaye shaye a tsakanin matasan jahar Katsina, jahar da yake rike da mukamin kwamishina a baya.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Wakili ya gaji tsohon kwamishinan Yansandan jahar Kano, Rabiu Yusuf, kuma yana daga cikin Yansandan da suka fara aiki a hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, a yanzu dai sauranshi watanni 3 ya yi murabus.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel