Gangamin PDP: Yan sanda sun kama yan yan daban siyasa 28 a Kano

Gangamin PDP: Yan sanda sun kama yan yan daban siyasa 28 a Kano

Rundunan yan sandan jihar Kano, ta bayyana a ranar Litinin. 11 ga watan Fabrairu cewa ta kama mutane 28 wadanda ake zargin yan bangan siyasa ne a yayinda jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ke gudanar da yakin neman zaben shugabancin kasa a jihar.

Sabon kwamishinan yan sanda a jihar, Mista Waikili Muhammad wanda ya kama aiki a ranar Litinin ne ya bayyana hakan, yayinda yake zantawa da manema labarai a Kano.

Gangamin PDP: Yan sanda sun kama yan yan daban siyasa 28 a Kano

Gangamin PDP: Yan sanda sun kama yan yan daban siyasa 28 a Kano
Source: Twitter

"A lokacinda na koma bakin aiki, wani lamari ya auku a ranar Lahadi, 10 ya watan Fabrairu yayinda ake gudanar da gangamin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP .

“Wasu mutane sun dauki doka a hannunsu; wanda ya janyo asaran dukiyoyi" inji shi.

Ya bayyana cewa ana cigaba da yin bincike don tabbatar da cewa masu hannu cikin lamarin sun fuskanci hukunci, inda ya kara da cewa “babu Wanda yafi karfin doka.

KU URANTA KUMA: Jirgin sojin Najeriya ya shafe sansanin horar da yan ta’adda a jihar Borno

“Kada Wanda yayi amfani da yaran talakawa a matsayin yan bangan siyasa yayinda nasu yayan basu kasance daga cikin masu daukar makamai ba.

“Ina muku kashedi; Ina mai tabbatarwa mutanen Kano cewa rundunan yan sanda bata daga cikin kowace jam’iyyar siyasa."

Haka zalika, shugaban yan sandan yayi kira ya shuwagabannin addinai, masu ruwa da tsaki, iyaye, maza da mata a jihar da su hada hannu don yaki da miyagun kwayoyi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel