Da alamun Walter Onnoghen ya kusa taba kasa, NJC ta kara mika masa takardan zargi

Da alamun Walter Onnoghen ya kusa taba kasa, NJC ta kara mika masa takardan zargi

Majalisar Koli ta shari'a NJC ta sake mikawa Jastis Walter Onnoghen, sabon takardan zargi kuma ana bukatan ya bada amsa akansu.

Bayan ganawarsu a ranan Litinin, majalisar ta bukaci Onnoghen ya amsa tambayoyi da zarge-zargen da hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC tayi masa.

Kafin karashe zaman, majalisar ta baiwa Walter Onnoghen kwanaki bakwai domin amsa wadannan zarge-zarge. Kana an nada sabuwar kwamitin gudanar da bincike kan tuhumar da akayiwa sabon Alkalin alkalai, Mohammed Tanko.

KU KARANTA: Yadda aka tarbi shugaba Buhari a jihar Bukola Saraki

Kakakin majalisar NJE, Soji Oye yace: "Majalisar ta sake zama a yau domin duba amsoshin da Mr. Justice W.S.N. Onnoghen, GCON da Mr. Justice I.T. Muhammad, suka basa bisa ga tambayoyi zargi ukun da aka rubuta musu.

"Kana majalisar ta samu sabuwar takarda daga hukumar EFCC kan Jastis Walter Onnoghen kuma an bukaci ya amsa cikin kwanaki bakwai."

"Majalisar ta amince da Jastis Umaru Abdullahi, ya cigaba da jagorantan majalisar kuma za'a sake wata zama ranan Laraba, 1 ga watan Febrairu, 2019."

Da alamun Walter Onnoghen ya kusa taba kasa, NJC ta kara mika masa takardan zargi

Da alamun Walter Onnoghen ya kusa taba kasa, NJC ta kara mika masa takardan zargi
Source: Twitter

Mun kawo muku a baya cewa Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta gano kudi $30,000 da wani babban lauya Joe Agi ya tura asusun bankin Jastis Walter Onnoghen, shugaban alkalan Najeriya da Buhari ya sallama.

Ya kara bayyana cewa Onnoghen bai bayyana wata asusun banki da ya mallaka a Heritage Bank ba, wani karin sabawa dokar Najeriya.

Joe Agi na daya daga cikin lauyoyin da ke tsayawa Walter Onnoghen a gaban kotun CCT.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel