Yanzu Yanzu: INEC ta fitar da samfurin kuri'u da akwatunan zabe, hotuna

Yanzu Yanzu: INEC ta fitar da samfurin kuri'u da akwatunan zabe, hotuna

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta fitar da samfurin kuri'u da akwatunan zabe gabannin zaben Shugaban kasa da na yan majalisar dokokin tarayya da za a gudanar a ranar Asabar, 16 ga watan Fabrairu.

Legit.ng ta rahoto cewa hukumar zaben c eta sanar da hakan a shafinta na twitter a ranar Litinin, 11 ga watan Fabrairu.

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) tace ta jajirce wajen koyon gudanarwa mafi inganci daga kasashen duniya domin inganta gudanarwar zaben kasar.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Takubu ne ya bayar da tabbacin lokacin da ya karbi bakuncin kungiyar masu lura da zabe karkashin jagoranin tsohon shugaban kasar Tanzania, Dr Jakaya Kikwete, a hedkwatar hukumar da ke Abuja a ranar Litnin.

KU KARANTA KUMA: Jirgin sojin Najeriya ya shafe sansanin horar da yan ta’adda a jihar Borno (bidiyo)

Yakubu yace sanya idanu daga kungiyar masu lura na kasasen duniya zai taimaka wa hukumar wajen inganta zabenta.

Bugu da kari, hukumarta bayyana kwarin guwar da ta ke da shi a kan sabbin na’urorin tantance ma su zabe da za a yi amfani da su a zabukan shekarar 2019 da za a fara a karshen makon nan da mu ke ciki.

A wata da aka yi da Mista Festus Okoye, kwamishina a INEC sannan shugaban kwamitin wayar da kan ma su zabe, ranar Asabar a Abuja ya ce yana da yakinin cewar na’urorin na da inganci kwarai da gaske.

Okoye ya bayyana cewar an inganta na’urorin tantancewar domin samun damar yin aiki cikin natsuwa da karancin matsaloli.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel