Wani mutum yayi barazanar kashe kansa idan shugaba Buhari bai yi nasara a zabe ba

Wani mutum yayi barazanar kashe kansa idan shugaba Buhari bai yi nasara a zabe ba

- Wani dan Najeriya ya nuna irin so da yakewa shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Adamu Kabir Matazu yayi barazanan kashe kansa idan Shugaban kasa Muhammadu Buhari bai lashe zaben shugaban kasa ba

- Matazu ya bayyana cewa ba zai iya rayuwa ba a karkashin shugabancin Atiku Abubakar

Wani dan Najeriya ya bayyana goyon bayansa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben shugaban kasa na 2019 a shafinsa na zumunta.

Mutumin ya bayyana hukuncin da ya tanadarwa kansa idan Shugaban kasa Buhari bai lashe zabe ba. Adamu Kabir Matazu ya bayyana shirinsa a shafinsa na Facebook inda ya yayi barazanar kashe kansa idan har Shugaban kasa Buhari bai lashe Zabe ba.

Matazu yayi ikirarin cewa ba zai iya rayuwa ba a karkashin dan takaran shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP)Atiku Abubakar ba.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Rikici ya barke a gangamin APC Ogun

Ya bayyana cewa zai kashe kansa kafin ranan Laraba, 29 ya watan Mayu, wato ranar da za a rantsar da sabon shugaban kasa idan har Buhari bai kai labari ba.

“Idan Buhari bai lashe zaben shugaban kasa da za a gudanar a ranar 16 ga watan Fabrairu ba, toh zan kashe kaina kafin 29 ya watan Mayu saboda bazan iya rayuwa ba a karkashin shugabancin Atiku. Taimake ni ya Ubangiji.” A cewar shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel