Fusatattun matasa sun tilasta tashin taron kamfen din Buhari a Ogun

Fusatattun matasa sun tilasta tashin taron kamfen din Buhari a Ogun

Rahotanni sun bayyana cewar an samu yawaitar ihun nuna rashin goyon baya daga jama’ar da su ka halarci taron kaddamar da yakin neman zaben jam’iyyar APC da shugaba Buhari ya kaddamar a jihar Ogun.

Majiyar mu ta shaida ma na cewar tsautsayi ya ritsa da shugaba Buhari a yayin wasu fusatattun matasa da su ka halarci taron kamfen din su ka hau jifa a lokacin da zai daga hannun dan takarar gwamnan jihar a karkashin tutar jam’iyyar APC.

Hargitsin ya fara ne a daidai lokacin da shugaba yah au kan munbari domin gabatar da jawabi.

Duk da matasan na ta yin ihu a wurin taron, sun yi shewar jinjina ga Buhari a lokacin da ya lissafo nasarorin da gwamnatin APC ta samu tare da fada ma su cewar su zabi duk dan takarar da su ke so a zabe mai zuwa.

Daga hannun dan takara: An jefi Buhari a jihar Ogun

Buhari a wurin kamfen
Source: UGC

Ku na da ‘yancin zaben duk dan takarar da ku ke a ranar Asabar da kuma ranar 2 ga watan Maris. Babu matsala a yin hakan,” shugaba Buhari ya shaida wa matasan da ke shewar jinjina gare shi.

Sai dai, matasan sun koma ihun nuna adawa a daidai lokacin da shugaba Buhari zai daga hannu da bayar da tuta gad an takarar gwamna a jihar, Dapo Abiodun.

DUBA WANNAN: Dalilin da ya sa mutanen jihar Legas ba za su zabi Atiku ba – Tinubu

Matasan sun fara jifa a lokacin da aka umarci Abiodun ya dawo daga bangaren damar shugaba Buhari domin ya daga hannun sa a matsayin dan takarar da yak e so jama’a su zaba a matsayin gwamnan jihar Ogun.

Fusatattun matasa sun hau yin jifa da abubuwa zuwa kan munbarin da shugaba Buhari tare da ragowar manyan jam’iyyar APC ke tsaye.

Jami’an tsaro sun gaggauta kange shugaban kasa don kar jifan ya same shi.

Haka taron kamfen din ya tashi babu girma, babu arziki.

Jihar Ogun dai na daga cikin jihohin da jam’iyyar APC ke fama da rikici tun bayan kamma zabukan fidda ‘yan takarar gwamna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel