Hargitsi yayin taron yakin zabe Buhari, Mutane 3 sun shiga hannu

Hargitsi yayin taron yakin zabe Buhari, Mutane 3 sun shiga hannu

- Mutane 3 sun shiga hannu daura da harabar filin wasanni ta MKO Abiola da ke birnin Abeokuta na jihar Ogun

- Ana zargin su da ta'addanci na karnukan siyasa yayin da shiga hannu da miyagun makamai da layu

- Ababen zargin sun shiga hannu yayin da suka yi yunkurin afkawa filin wasannin da aka tanada domin taron yakin zaben Buhari

Mun samu cewa, wasu mutane uku da ake zargin su da ta'addanci irin na karnukan siyasa sun shiga hannun jami'an tsaro gabanin taron yakin neman zabe na shugaban kasa Muhammadu Buhari a filin wasanni na MKO Abiola da ke birnin Abeokuta na jihar Ogun.

Hargitsi yayin taron yakin zabe Buhari, Mutane 3 sun shiga hannu

Hargitsi yayin taron yakin zabe Buhari, Mutane 3 sun shiga hannu
Source: Original

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, ababen zargin uku sun shiga hannu tare da miyagun makamai da kuma layu na siddabaru yayin da suka yi yunkurin afkawa harabar filin wasanni na Abiola inda shugaba Buhari zai gudanar da taron sa na yakin zabe.

Rahotannin sun bayyana cewa, miyagun uku sun shiiga hannu tun gabanin isowar shugaban kasa Buhari yayin da tuni harabar ta dinke makil da dumbin al'umma tamkar tururuwa domin jaddada goyon baya.

KARANTA KUMA: 2019: Buhari zai ci zabe da kaso 60% na kuri'u - Rahoto

Kamar yadda shafin jaridar The Punch, jami'an tsaro da suka hadar da 'yan sanda, DSS, dakarun soji da jami'an tsaro na Civil Defense sun yi tsayuwar daka tare da kai komo na sinitiri domin tabbatar da tsaro da ya rataya a wuyan su.

A yayin haka tuni dai jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a yau Litinin 11 ga watan Fabrairu, shugaban kasa Buhari zai gudanar da taron sa na yakin zabe a jihar Ogun da kuma Kwara, inda a jiya Lahadi ya gudanar da taron sa na yakin zabe cikin birnin Gusau na jihar Zamfara.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel