Buhari bai da lokacin da zai bata yana rubutawa Obasanjo wasika – Fashola

Buhari bai da lokacin da zai bata yana rubutawa Obasanjo wasika – Fashola

Mun samu labari cewa babban ministan Najeriya, Raji Babatunde Fashola, ya caccaki tsohon shugaban kasar Najeriya Cif Olusegun Obasanjo a dalilin sukar gwamnatin shugaba Buhari da ya saba yi.

Buhari bai da lokacin da zai bata yana rubutawa Obasanjo wasika – Fashola

Ministan ayyuka da titunan Najeriya yace a fada a cika sai Buhari
Source: UGC

Ministan na ayyuka da gidaje da kuma wutan lantarki na Najeriya, ya maidawa Olusegun Obasanjo martani ne a Ranar Asabar din da ta wuce a game da wasikun da yake rubutawa game da shugaban kasa Muhammadu Buhari bini-bini

Fashola yayi wannan magana ne a wajen yakin neman zaben da jam’iyyar APC mai mulki ta gudanar a jihar Legas inda yayi kira ga Yarbawa su yi watsi da maganar Obasanjo su sake marawa Buhari baya a wani karo a babban zaben bana.

KU KARANTA: APC sun gano mugun nufin su Atiku a kan Buhari daf da zabe

Tunde Fashola wanda tsohon gwamna ne a Legas yake fadawa jama’a cewa shugaba Buhari bai da lokacin zama yana rubuta wasika domin yi wa wani raddi. Ministan yake cewa Buhari ba mutum bane mai surutu sai da kurum a ga aiki.

Mista Raji Fashola yayi murna da shugaban kasar ya zo har Mahaifar sa ta Surulere inda yace nan ne Daurar sa a Legas. Ministan ya kuma lissafo kadan daga ayyukan gwamnatin Buhari wanda su ka hada da kamfanoni da ayyukan wuta.

Ministan na lantarki yace shugaba Buhari na kokarin kammala aikin Mambilla, da kuma tada kamfanoni tare da gina hanya tun daga cikin Apapa har zuwa garin Oworonshoki a jihar ta Legas.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel