Yanzu Yanzu: Rikici ya barke a gangamin APC Ogun

Yanzu Yanzu: Rikici ya barke a gangamin APC Ogun

Jami’an tsaro sun kare Shugaban kasa Muhammadu Buhari lokacin da wani rikici ya barke a gangamin kamfen din Shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Ogun a ranar Litinin, 11 ga watan Fabrairu.

Rikici ya barke a gangamin kamfen din jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da ke gudana a Abeokuta.

Shugaban kasar bai iya kaiwa karshen jawabinsa ba a filin wasa na MKO Abiola, Abeokuta, inda dandazon jama’a suka taru.

Rikicin ya fara ne a lokacin da shugaba Buhari ya daga hannun Dapo Abiodun, dan takarar gwamnan jam’iyyar PDP a jihar.

Yanzu Yanzu: Rikici ya barke a gangamin APC Ogun

Yanzu Yanzu: Rikici ya barke a gangamin APC Ogun
Source: Original

Nan take sai wasu fusatattun mutane suka fara jifan abubuwa a inda Shugaban kasar yake, akan ya tursasa jami’an tsaro yin zobe a kewaye da shi.

Da farko daman fusatattun mutanen sun fara ifan Adams Osiomole, Shugaban APC na kasa da duwatsi sannan suka fatattaki magoya bayan Abiodun daga filin taron.

An tattaro cewa kamfen din ya dauki sabon sauyi lokacin da gwamnan jihar, Ibikunle Amosun ya hau kan munbari don yiwa APC da Allied Peoples Movement (APM) kamfen.

KU KARANTA KUMA: Zaben 2019 zai zamo zabena na 5 kuma na karshe, ba zan wofantar da kundin tsarin mulki ba - Buhari

Don mayar da martani, sai tsohon gwamna Aregbesola ya hau kan manbari don nuna adawa ga gwamnan, inda ya bukaci mutane da su zabi yan takarar jam’iyyar All Progressives Congress mai mulki kadai.

Bayan Aregbesola ya fara Magana, sai magoya bayan APM suka nuna turjiya ta fatar baki sannan sai hakan ya haifar da hayaniya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel