Jirgin sojin Najeriya ya shafe sansanin horar da yan ta’adda a jihar Borno (bidiyo)

Jirgin sojin Najeriya ya shafe sansanin horar da yan ta’adda a jihar Borno (bidiyo)

Rundunar sojojin saman Najeriya na Operation lafiya dole ta shafe sansanin horar da yan ta’addan ISWAP sannan ta kase yan ta’adda da dama a Malkonory da ke arewacin jihar Borno.

An gudanar da aikin kakkaban ne a jiya Lahadi, 10 ga watan Fabrairu, bayan shafin kwararru sun gano ayyukan mutane da dama a yankin, da kuma kayayyaki da motoci da taimakon jirgin yaki.

Yan ta’addan na amfani da sansanin ne wajen horar da mabiyanta.

Rahoto ya nuna cewa anyi amfani da jiragen yaki biyu ne waen kaddamar da hari a wurin, sannan sunyi nasarara ajiye bama-bamai a wajen inda ya kama da wuta wanda yayi sanadiyar kashe yan ta’addan da dama.

Rundunar ta jadadda aikin da take yi wajen ganin tayi nasarar halaka sauran yan ta’addan a arewa maso gabas.

KU KARANTA KUMA: Zaben 2019 zai zamo zabena na 5 kuma na karshe, ba zan wofantar da kundin tsarin mulki ba - Buhari

A halin da ake ciki mun ji labari cewa shugaban hafsun sojin Najeriya Janar Tukur Yusuf Buratai, ya bayyana cewa zai yi kokari wajen ganin ya rusa hadin-gwiwar da aka samu tsakanin ‘Yan ta’addan Boko Haram da kuma Takwaran su na ISWA.

Laftana Janar Tukur Buratai yayi wannan jawabi ne dazu a Abuja wajen wani taron kwana 2 da aka shiryawa manyan sojojin Najeriya. Janar Buratai ya kuma bayyana cewa su na samun galaba a kan ‘yan ta’addan Boko Haram.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel