Tsohon Shugaban kasa IBB ya bayyana matsayarsa akan zaben ranar Asabar mai zuwa

Tsohon Shugaban kasa IBB ya bayyana matsayarsa akan zaben ranar Asabar mai zuwa

- Tsohon shugaban kasar Najeriya, Ibrahim Babangida ya yi kira ga al’umman kasar da su yi amfani da hankulansu wajen zaben shugabanninsu

- Ya nemi su zabi shugabanni da za su wanzar da zaman lafiya mai dorewa a kasar

- IBB yace babban burinsa shine ganin an yi zabe cikin zaman lafiya

Tsohon shugaban kasar Najeriya a mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (mai ritaya), ya yi kira ga al’umman kasar da su yi amfani da hankulansu wajen zaben shugabannin da za su kawo zaman lafiya mai dorewa a kasar.

A wata hira da ya yi da manema labarai, IBB ya ce ba shi da fatan da ya wuce na ganin an yi zabe cikin kwanciyar hankali da lumana.

Ya ce 'yan takara sun sanya hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya bayan zabe, kuma ya na fatan kowanne bangare zai mutunta hakan da kuma gujewa musayar munanan kalamai.

Tsohon Shugaban kasa IBB ya bayyana matsayarsa akan zaben ranar Asabar mai zuwa

Tsohon Shugaban kasa IBB ya bayyana matsayarsa akan zaben ranar Asabar mai zuwa
Source: UGC

Janar Babangida, ya ce babu wanda ya ke goyon-baya ko zai umarci 'yan kasar su zaba sai dai ya na fatan a yi zabi nagari.

KU KARANTA KUMA: Atiku ya ci zaben ranar 16 ga watan Fabrairu ya gama – Gbenga Daniel

Tsohon shugaban ya kuma ce, yanzu kan mutane ya waye, kowa ya san 'yanci don haka baya ji a yanzu za iya amfani da kudi wajen sayen kuri'a don haka yana da yakinin cewa za ayi zabe bisa ga cancanta.

A wani lamari na daban, mun ji cewa dan majalisa mai wakiltar al’ummar mazabar Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa idan har shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gagara samun nasara a zaben 2019, ta tabbata rugujewar jam’iyyar APC ya fara kenan.

Shehu Sani ya bayyana haka ne cikin wata hira da yayi da jaridar Premium Times, inda yayi nuni da tasirin jam’iyyar APC ta tattara ne ga nasarar shugaban kasa Buhari a zaben ranar 16 ga watan Feburairun shekarar 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel