Zaben 2019 zai zamo zabena na 5 kuma na karshe, ba zan wofantar da kundin tsarin mulki ba - Buhari

Zaben 2019 zai zamo zabena na 5 kuma na karshe, ba zan wofantar da kundin tsarin mulki ba - Buhari

- Shugaban kasa Buhari, ya yiwa yan Najeriya alkawarin cewa zaben ranar 16 ga watan Fabrairu shine zaben karshe da zai gudanar

- Buhari ya sha alwashin cewa wannan shine zabensa na biyar kuma na karshe, inda ya kara da cewa bayan wannan ba zai sake takara ba

- Dan takarar na APC ya bukaci shugabannin gargajiya da suyi iya bakin kokarinsa don hana sace-sacen mutane da fashi da makami a yankinsu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Lahadi, 10 ga watan Fabrairu ya yiwa yan Najeriya alkawarin cewa zaben ranar 16 ga watan Fabrairu shine zaben karshe da zai gudanar.

A jawabinsa ga sarakunan gargajiya a gidan gwamnati da ke Abuja, shugaba Buhari ya sha alwashin cewa wannan shine zabensa na biyar kuma na karshe, inda ya kara da cewa bayan wannan ba zai sake takara ba, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Zaben 2019 zai zamo zabena na 5 kuma na karshe, ba zan wofantar da kundin tsarin mulki ba - Buhari

Zaben 2019 zai zamo zabena na 5 kuma na karshe, ba zan wofantar da kundin tsarin mulki ba - Buhari
Source: UGC

Sannan kuma ya bukaci shugabannin gargajiya da suyi iya bakin kokarinsa don hana sace-sacen mutane da fashi da makami a yankinsu, inda ya kara da cewa bai ji dadin yadda yaji cewar wasu da ke aikata laifukan na kusa da sune.

KU KARANTA KUMA: Wasu manyan jiga-jigan APC sun sauya sheka zuwa PDP a Plateau

A wani lamari na daban, mun ji cewa Tsohon gwamnan jihar Ogun kuma mataimakin shugaban kungiyar kamfen din dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Gbenga Daniel a ranar Lahadi, 10 ga watan Fabrairu ya kaddamar da cewar Atiku Abubakar ya rigada ya ci zaben ranar 16 ga watan Fabrairu ya gama.

Daniel, ya bayar da tabbacin ne yayinda yake amsa tambayoyi daga manema labarai a Ijebu Ode,jiar Ogun jim kadan bayan y agama jawabi ga magoya bayan jam’iyyar PDP daga cikin rangajin kamen da suke yi a yankin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel