2019: Buhari zai ci zabe da kaso 60% na kuri'u - Rahoto

2019: Buhari zai ci zabe da kaso 60% na kuri'u - Rahoto

A yayin da rage sauran kwanaki biyar kacal a gudanar da babban zaben kasa a ranar Asabar,16 ga watan Fabrairu, wata babbar cibiyar duniya mai nazari da bincike akan harkokin siyasa dake kasar Amurka, ta yi hasashen yadda sakamkon zaben Najeriya zai kasance.

Sakamakon kididdigar da cibiyar nazari da kiyasi akan harkokin siyasa dake birnin New York na kasar Amurka ta fitar a ranar 7 ga watan Fabrairu, ta bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari za ya lashe babban zabe na ranar Asabar da kimanin kaso sittin cikin dari na kuri'un da za a kada.

Cibiyar mai lakabin Eurasia group da ta shahara wajen daukar nauyin gudanar da bincike da kuma tuntube-tuntube gami da shawarwari akan harkokin siyasa cikin kimanin kasashe 100 da ke fadin duniya, ta ce nasara ta na ga shugaba Buhari a zaben bana.

2019: Buhari zai ci zabe da kaso 60% na kuri'u - Rahoto

2019: Buhari zai ci zabe da kaso 60% na kuri'u - Rahoto
Source: UGC

Eurasia ta ce, mashahurancin dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ba za ya yi tasiri ba wajen tabbatar da nasarar sa a zaben bana sakamakon rashin ingantaccen goyon baya da ya gaza samu a jam'iyyar sa.

KARANTA KUMA: Cikin kwanaki 2 an kashe Mutane 21 a Birnin Gwari - Shehu Sani

A yayin da nasarar shugaba Buhari na da nasaba da mafi rinjayen adadin gwamnoni na jam'iyyar APC a fadin kasar nan, Atiku ya gaza samun goyon baya matabbaci musamman a bangaren jagoran kungiyar yakin neman zaben sa, Abubakar Bukola Saraki.

Masu sharhi akan siyasa sun bayyana cewa, hankalin Saraki ya rabu gida biyu sakamakon yadda ya ke ci gaba da hankoron komawa bisa kujerar sa ta shugaban Majalisar dattawa a matsayin wakilin Sanatan shiyyar Kwara ta Tsakiya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel