Atiku ya ci zaben ranar 16 ga watan Fabrairu ya gama – Gbenga Daniel

Atiku ya ci zaben ranar 16 ga watan Fabrairu ya gama – Gbenga Daniel

- Tsohon gwamnan jihar Ogun Gbenga Daniel ya kaddamar da cewar Atiku Abubakar ya rigada ya ci zaben ranar 16 ga watan Fabrairu ya gama

- Daniel ya bayyana cewa ya tattara daga zantawarsa da yan Najeriya wadanda suka fallasa asirin zuciyarsu cewa babu shakka sun yi kuskuren zabar jam’iyyar APC mai mulki a zaben 2015

Tsohon gwamnan jihar Ogun kuma mataimakin shugaban kungiyar kamfen din dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Gbenga Daniel a ranar Lahadi, 10 ga watan Fabrairu ya kaddamar da cewar Atiku Abubakar ya rigada ya ci zaben ranar 16 ga watan Fabrairu ya gama.

Daniel, ya bayar da tabbacin ne yayinda yake amsa tambayoyi daga manema labarai a Ijebu Ode,jiar Ogun jim kadan bayan y agama jawabi ga magoya bayan jam’iyyar PDP daga cikin rangajin kamen da suke yi a yankin.

Atiku ya ci zaben ranar 16 ga watan Fabrairu ya gama – Gbenga Daniel

Atiku ya ci zaben ranar 16 ga watan Fabrairu ya gama – Gbenga Daniel
Source: Depositphotos

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa ya tattara daga zantawarsa da yan Najeriya wadanda suka fallasa asirin zuciyarsu cewa babu shakka sun yi kuskuren zabar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a zaben 2015 inda suka bayyana cewa za su gyara wannan kuskuren ta hanyar zabar PDP a zaben ranar Asabar mai zuwa.

KU KARANTA KUMA: Wasu manyan jiga-jigan APC sun sauya sheka zuwa PDP a Plateau

Daniel wanda ya ga laifin jam’iyya mai mulki kan gurbata tattalin arziki, rashin tsaro, yawan rashin aikin yi a kasar, ya bayyana cewa sugabancin Atiku zai dawo da albarkatun kasar da kuma abbaka tattalin arziki idan har aka zabe shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel