Matukar Buhari ya fadi zaben 2019, APC ta mutu murus – Shehu Sani

Matukar Buhari ya fadi zaben 2019, APC ta mutu murus – Shehu Sani

Dan majalisa mai wakiltar al’ummar mazabar Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa idan har shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gagara samun nasara a zaben 2019, ta tabbata rugujewar jam’iyyar APC ya fara kenan.

Shehu Sani ya bayyana haka ne cikin wata hira da yayi da jaridar Premium Times, inda yayi nuni da tasirin jam’iyyar APC ta tattara ne ga nasarar shugaban kasa Buhari a zaben ranar 16 ga watan Feburairun shekarar 2019.

KU KARANTA: Kanal Sagir Musa ya zama sabon Kaakakin rundunar Sojan kasa

Matukar Buhari ya fadi zaben 2019, APC ta mutu murus – Shehu Sani

Buhari da Shehu Sani
Source: UGC

“Yan siyasan dake komawa cikin jam’iyyar APC sun kashi uku, akwai wadanda suke komawa saboda su tsira daga shari’a, akwai wadanda suke komawa saboda talauci, wasu kuma suna komawa ne saboda ba zasu iya rayuwa ba a cikin jam’iyya mai mulki ba.

“Ina tabbatar muku idan Buhari ya lashe zaben 2019, tabbas PDP ta mutu kenan saboda yayan jam’iyyar PDP da dama zasu gudu su koma cikin APC, amma idan kuma Buhari ya fadi zaben 2019, tabbas APC ta mutu ita ma murus, domin yayanta da dama zasu koma cikin PDP.” Inji shi.

Sai dai Sanatan ya bayyana wata babbar kalubale da jihohin Arewacin Najeriya guda goma sha tara zasu fuskanta idan har Buhari ya lashe zabe a shekarar 2019, kuma yankin kudancin Najeriya suka karbi mulki a shekarar 2023.

Wannan kalubale da Sanatan yayi nuni da ita itace batun sauyin fasalin Najeriya, wanda jama’an yankin kudancin kasarnan suke ta rurutawa wajen neman an tabbatar da shi, a cewar Sanatan, Jihohin Arewacin Najeriya 19 basu shirya ma sauyin fasalin kasar ba.

Da yake tsokaci kan rigimarsa da gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa El-Rufai a matsayin mutumin dake cin gajiyar farin jinin shugaban kasa Muhammadu Buhari, kuma duk kuri’ar daya samu saboda Buhari ya sameta.

Amma yace shi kam dan siyasane mai cin gashin kansa, baya bukatar jingina da wani dan siyasa kafin ya samu kuri’u, don haka yayi kira ga gwamnan daya fito su buga shi da shi kadai, ya gani idan jama’a na don Buhari suke sonsa ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel