Tura ta kai bango: Jama’an gari sun halaka yan bindiga guda 5 a jahar Katsina

Tura ta kai bango: Jama’an gari sun halaka yan bindiga guda 5 a jahar Katsina

A duk lokacin da jama’a suka hada kansu, suka zamto tamkar tsintsiya madaurinki daya, toh daga wannan lokaci babu wanda ya isa ya juyasu yadda yake so, ko ya yi musu dole ko kuma ya zalunceshi face sun tunkareshi, har sai sun ci karfinsa.

Dama masu iya magana na cewa “Sarkin yafi sarkin karfi”, anan wasu gungun masu garkuwa da mutane ne suka gamu da bazata daga hannun jama’a kauyen Gidan Garkuwa dake cikin karamar hukumar Sabuwa ta jahar Katsina, inji rahoton Daily Trust.

KU KARANTA: Kanal Sagir Musa ya zama sabon Kaakakin rundunar Sojan kasa

Su dai wadannan yan bindiga da aka bayyana adadinsu ya kai mutum ashirin sun far ma kauyen ne da nufin yin dauki daidai kamar yadda suka saba, har sai an biyasu kudin fansa, sai dai jama’an garin sun nuna jarumta, inda suka fuskancesu, har suka kashe mutane biyar daga cikinsu.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a ranar Lahadi, 10 ga watan Feburairu da misalin karfe 1 na dare, a lokacin da yan bindigan sika isa kauyen, inda suka fara harbe harbe a iska da nufin tsoratar da jama’an.

“Ba tare da bata lokaci ba suka afka gidan Alhaji Tanimu Maitaken Naira inda suka dauke wata mata da diyarta, ana cikin haka ne sai wasu gungun fusatattun matasa suka fuskanci yan bindigan, nan take suka kashe mutane biyar daga cikinsu, yayin da sauran suka ranta ana kare.” Inji shidan gani da ido.

Sai dai kaakakin Yansandan jahar Katsina, SP Gambo Isah ya bayyana ma majiyarmu cewa lamarin ya faru ne a kauyen Yartukunya, sa’annan yace mutane uku kacal aka kashe da suka hada da Alhaji Bello, Nagagara, dukansu masu garkuwa da mutane ne, sai kuma wani guda da ba’a bayyana sunansa ba.

Daga karshe SP Gambo yace sun samu nasarar ceto matar da yan bindigan suka yi garkuwa da ita, sa’annan yace sai bayan yan bindigan sun gama dauke daukensu, har ma sun nufi shiga daji ne matasan suka cimmasu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel