16 ga watan Fabrairu: APC ta kira taro na musamman

16 ga watan Fabrairu: APC ta kira taro na musamman

Yayinda kamfen din takarar shugabancin kasa ke zuwa karse a wannan makon, jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a daren ranar Lahadi, 10 ga watan Fabrairu ta kira wani taro na mussamman a kokarinta na shirya manufofin karshe kafin zaben Shugaban kasa da na yan majalisar dokoki da za a yi a ranar 16 ga watan Fabrairu.

Taron wanda kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar ta kira ya samu alartan dukkanin sugabannin APC da sakatarorinsu, yan takarar gwamna da kuma na sanata.

An tattaro cewa ba a gayyaci yan takarar kujerar majalisar wakilai da na majalisar dokokin jiha ba zuwa wajen taron na mussamman.

16 ga watan Fabrairu: APC ta kira taro na musamman

16 ga watan Fabrairu: APC ta kira taro na musamman
Source: UGC

Baya ga tattaunawa kan kamfen din kasa da ke gudana, taron zai ba jam’iyyar damar magance lamura da dama da ke ci mata tuwo a kwarya ciki arda hukuncin kotun koli kan jam’iyyar reshen jihohin Rivers da Zamfara wanda har yanzu ke fuskantar kalubale wajen cike yan takararsu.

KU KARANTA KUMA: Yan takarar kujerar gwamna na APC 8 sun rubuta takarda ga majalisar alkalai kan rokon Yari

Hakazalika ana sanya ran za a yanke hukunci kan makomar gwamnan jihar Imo, Owelle Rochas Okorocha, wanda jam’iyyar reshen jihar ta dakatar dashi kwanakin baya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel