Wasu manyan jiga-jigan APC sun sauya sheka zuwa PDP a Plateau

Wasu manyan jiga-jigan APC sun sauya sheka zuwa PDP a Plateau

- Wasu manyan jami’an jam’iyyar APCda daruruwan magoya bayansu daga karamar hukumar Jos South na jihar Plateau sun sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP

- Mai ba APC shawara akan doka, Hon. Joseph Mani, wanda ya jagoranci masu sauya shekar ya bayyana cewa sun bar APC ne saboda jam’iyyar bata da abun ba yan Najeriya

- Ya bayyana cewa shugabancin Atiku ne mafita ga kasar

Wasu manyan jami’an jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da daruruwan magoya bayansu daga karamar hukumar Jos South na jihar Plateau sun sauya sheka zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) domin hadewa da Shugaban kwamitin doka da kasuwanci a majalisar wakilai, Hon. Edward Pwajok (SAN).

Mai ba APC shawara akan doka, Hon. Joseph Mani, wanda ya jagoranci masu sauya shekar ya bayyana cewa sun bar APC ne saboda jam’iyyar bata da abun ba yan Najeriya.

Wasu manyan jiga-jigan APC sun sauya sheka zuwa PDP a Plateau

Wasu manyan jiga-jigan APC sun sauya sheka zuwa PDP a Plateau
Source: UGC

Yace: “Mun koma PDP ne don marawa Hon. Edward Pwajok wajen kawo wa Atiku Abubakar, dan takarar Shugaban kasa a PDP, dan takarar gwamna na jam’iyyar Sanata Jeremiah Useni, da kuma dukkanin yan takarar PDP kuri’u da yawa a jihar Plateau.

“Mun yi ammana cewa shugabancin Atiku da Useni a matsayin gwamna a jihar Plateau, zai inganta rayuwar yan Najeriya sannan ya kawo zaman lafiya ta yadda yan gudun hijira a jihar Plateau za su koma gidajensu. APC babu komai cikinta sai tarin yaudar, a kullun suna cikin korafi saboda jam’iyyar bata da abun nunuwa."

KU KARANTA KUMA: Yan takarar kujerar gwamna na APC 8 sun rubuta takarda ga majalisar alkalai kan rokon Yari

Pwajok yace idan aka zabi Atiku, yunwa, rashin tsaro da koma bayan tattalin arziki duk za su zamo labara sannan naira zai dawo da daraja, yayinda tattalin arzikin Najeriya zai inganta.

Wani tsoon ministan matasa da wasanni da kuma Shugaban PDP a jihar Platau, Hon. Damishi Sango, wanda ya tarbi masu sauya shekar a karamar hukumar Barkin Ladi da ke jihar Plateau, yace PDP ce kadai jam’iyyar da ta damu da tsaro da jin dadin mutanen Plateau.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel