2019: Ranar Asabar Buhari zai fadi zabe - Inji Uche Secondus

2019: Ranar Asabar Buhari zai fadi zabe - Inji Uche Secondus

- Prince Uche Secondus yace APC za ta sha kashi a babban zabe mai zuwa

- Shugaban Jam’iyyar PDP na Najeriya yace Buhari zai koma Kauyen sa

- Secondus yana cika bakin PDP za ta fatattaki Shugaba Buhari zuwa Daura

2019: Ranar Asabar Buhari zai fadi zabe - Inji Uche Secondus

PDP ta na ganin Buhari zai sha kashi a zaben Shugaban kasa
Source: Twitter

Labari ya iso gare mu cewa Shugaban babbar jam’iyyar adawa ta Najeriya watau PDP yace shugaba Muhammadu Buhari zai fadi zaben da za ayi kwanan nan. A karshen makon nan ne za ayi zaben shugaban kasa a Najeriya.

Shugaban jam’iyyar PDP din na kasa baki daya, Prince Uche Secondus ya bayyana cewa a Ranar Asabar dinnan ne jama’an Najeriya za su zabi jam’iyyar PDP inda za a tika APC mai mulki daga kasa a zaben shugaban kasa da za ayi.

KU KARANTA: APC sun bankado mugun nufin PDP game da Shugaba Buhari

Uche Secondus yayi wannan jawabi ne a shafin sa na sadarwa na Tuwita bayan ganin irin lale marhabin din da dinbin jama’a su ka yi wa ‘dan takarar PDP na shugaban kasa watau Atiku Abubakar a jihar Kano jiya Ranar Lahadi.

Secondus yace kwanakin baya mutane sun amsa kiran Atiku Abubakar a Katsina inda nan shugaban kasa ya fito, sannan kuma ya ga yadda Kanawa kwan-su da kwarkwatar su, su ka ba jam’iyar hamayyar goyon baya a jiya.

Shugaban na PDP yake cewa irin watsi da jama’ar Legas su kayi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna cewa babu shakka PDP za tayi nasara yayin da shi kuma shugaba Buhari zai koma gida.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel