Siyasar Kano ta kazanta: An banka ma gidan Abba Kabir Yusuf wuta a Kano

Siyasar Kano ta kazanta: An banka ma gidan Abba Kabir Yusuf wuta a Kano

Yayin da babban zaben shekarar 2019 ke cigaba da karatowa, farfajiyar siyasar Najeriya na kara dumama, domin kuwa a yanzu haka abin ya haura dumama, har ta zafafa, kuma wannan shine babban abinda ake tsoro ya faru a siyasar.

A duk lokacin da aka ce siyasa ta yi zafi, za’a ga cewa abokan hamayya basa jituwa, hamayyar kanta ta sauya ta koma kiyayya kararara, sau dayawa hakan ka iya sabbaba asarar dukiya, da kuma asarar rayuka a sakamakon tashin hankalin da hakan ke haifarwa.

KU KARANTA: Dandalin Kannywood; Sanata Kwankwaso ya damka ma Adam Zango darikar Kwankwasiyya

Siyasar Kano ta kazanta: An banka ma gidan Abba Kabir Yusuf wuta a Kano

Gidan Abba
Source: Facebook

Da yammacin ranar Lahadi, 10 ga watan Feburairu ne wasu miyagun fusatattun matasa suka kai farmaki zuwa wani gida mallakin dan takarar gwamnan jahar Kano a inuwar jam’iyyar PDP, kuma jigo a tafiyar Kwankwasiyya, Injiniya Abba Kabir Yusuf, inda suka kone gidan kurmus.

Shi dai wannan gida yana nan ne a unguwar Chiranchi, kuma majiyar Legit.ng ta ruwaito Abba Yusuf ya gina wannan gida ne domin gudanar da tarukan siyasa, da na bukukuwa a cikinsa, a takaice dai jama’a ke amfani da gidan fiye da shi.

Siyasar Kano ta kazanta: An banka ma gidan Abba Kabir Yusuf wuta a Kano

Gidan Abba
Source: Facebook

Sai dai wasu masana siyasar Kano suna ganin kone gidan Abba baya rasa nasaba da nasarar da jam’iyyar PDP ta samu a gangamin yakin neman zaben Atiku Abubakar data gudanar a jahar Kano a ranar Lahadi a filin wasa na Sani Abacha.

Dubun dubatan al’ummma ne suka yi tururuwa tare da yin fitar farin dango zuwa filin wasan domin tarbar Atiku Abubakar da jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, wanda a dalilin haka wasu mutane bakwai suka fadi sumammu saboda tsabagen turmutsitsin jama’a.

Siyasar Kano ta kazanta: An banka ma gidan Abba Kabir Yusuf wuta a Kano

Gidan Abba
Source: Facebook

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel