Zabe: INEC ta koka game da lamarin gobara a ofishinta

Zabe: INEC ta koka game da lamarin gobara a ofishinta

- Hukumar zabe mai zaman kanta ta nuna damuwa game da lamarin gobara a ofishinta na karamar hukuma biyu

- Mista Festus Okoye, Shugaban kwamitin wayar da kan masu zabe ya ce hukumar ta sanar da Shugaban yan sanda, Moammed Adamulamarin da ke afkuwa

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta nuna damuwa game da lamarin gobara a ofishinta na karamar hukuma biyu.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa ofishin INEC da ke karamar hukumar Isiala Ngwa South a jihar Abiya ya kama gobara. Sannan kuma a daren ranar Asabar lamarin ya sake afkuwa a kramar hukumar Qua’an da ke jihar Plateau.

Zabe: INEC ta koka game da lamarin gobara a ofishinta

Zabe: INEC ta koka game da lamarin gobara a ofishinta
Source: UGC

“Wasu daga cikin abubuwan da suka salwana a gobarar na karamar hukumar Isiala Ngwa South sun hada da katunan zabe 2929 da sauran kayayyaki.

“A na karamar hukumar Qua’an kuma sun hada da dukkan akwatunan zaben da za a yi amfani da su, tulin katin rajista na dindindin da masu su ba su kai ga karba ba, rajistar da ke dauke da sunayen masu zabe na karamar hukumar da ke kan takarda da kuma na cikin kwamfuta."

KU KARANTA KUMA: NJC za ta dawo zama yau kan Onnogen da Muhammed

Mista Festus Okoye, Shugaban kwamitin wayar da kan masu zabe ya ce hukumar ta sanar da Shugaban yan sanda, Moammed Adamulamarin da ke afkuwa na kona ofisinta na kananan hukuma a lokacin da ake gab da fara zabe sannan kuma lokacin da hukumar ke kan ganiyar kai kayayyakin zabe a fadin kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel