Yan takarar kujerar gwamna na APC 8 sun rubuta takarda ga majalisar alkalai kan rokon Yari

Yan takarar kujerar gwamna na APC 8 sun rubuta takarda ga majalisar alkalai kan rokon Yari

Yan takarar kujerar gwamna a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Zamfara su takwas, sun soki yunkurin gwamnan jihar, Abdulaziz Yari na tursasa hukuncin babbar kotun jihar Zamfara akan yan takarar APC.

Yan takarar karkashin inuwar G-8, sunce gwamnan ya cika takardar kara, inda ya nemi a tursasa hukuncin babbar kotun jiar kan yan takarar wanda a cewarsu hakan bakon lamari ne ga doka.

Don haka, yan takarar wadanda suka hada da Sanata Kabir Garba Marafa, mataimakin gwamnan jiarm Malam Ibrahim Wakala, tsohon gwamnan jihar, Mahmud Aliyu Shinkafi, Ministan tsaro, Mansur Dan-Ali, dan majalisar wakilai Sani Jaji, Injiniya Magaji, Dauda Lawal da kuma Mohammed Sagir Hamidu, sunyi kira ga majalisar alkalai kan tayi gaggawar shiga lamarin.

Yan takarar kujerar gwamna na APC 8 sun rubuta takarda ga majalisar alkalai kan rokon Yari

Yan takarar kujerar gwamna na APC 8 sun rubuta takarda ga majalisar alkalai kan rokon Yari
Source: Twitter

Takwas daga cikin yan takarar sun kafa G-8, biyo bayan rikicin da ya taso a zaben fidda gwanin APC a jihar.

Wata kotun roko da ke zaune a Sokoto ta dage rokon yan takarar APC zuwa ranar 19 ga watan Fabrairu, 2019 domin ci gaba da shari’a. An yanke hukunci biyu a ranar 2 ga watan Janairu kan lamarin.

KU KARANTA KUMA: NJC za ta dawo zama yau kan Onnogen da Muhammed

Wata babbar kotun tarayya karkashin jagorancin Justis Ijeoma Ojukwu ta bayyana cewa INEC tayi aiki bisa ikonta na kin amincewa da jerin sunayen yan tara daga wani bangare na APC a jiar Zamfara.

Hukuncin na biyu Justis Muammed Bello Shinkafi na babbar kotu a Gusau, jihar Zamfara ne ya yanke sa. Shinkafi ya bayar da tabbacin cewa an gudanar da zaben fidda gwani sannan ya nemi INEC da ta amince da sunayen yan takarar da aka zamu daga zaben fidda gwanin. Bayan nazari akan hukuncin biyu, INEC ta yanke sawarar tsayawa kan matsayarta na farko akan lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel