Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya dira jihar Bukola Saraki

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya dira jihar Bukola Saraki

Shugaba Muhammadu Buhari ya dira jihar Kwara, mahaifar shugaban majalisar dattawa kuma diraktan yakin neman zaben Atiku Abubakar, Bukola Saraki, a ranan Litnin, 11 ga watan Febrairu, 2019 domin gudanar da yakin neman zabe.

Daga nan kuma zai garzaya jihar Ogun da rikici ya raba kan yan jam'iyyar APC domin karashe yakin neman zaben na yankin kabilar Yarabawa.

Legit ta samu wannan labari ne daga hadimin shugaba Buhari kan kafafan sada ra'ayi da zumunta, Bashir Ahmad, inda yace:

"Shugaba Buhari ya isa garin Ilori jihar Kwara domin yakin neman zabe. Zai karasa jihar Ogun daga baya domin cigaba."

A ranan Asabar da Lahadi, shugaba Muhammadu Buhari ya yi irin wannan taro a jihar Legas da jihar Zamfara inda ya samu kyakkyawan tarba, yayinda babban abokin hamayyarsa, Atiku Abubakar, kuma yayi nasa a jihar Kano.

Zaben dai ya gabata ana saura kwanaki 5 yanzu inda za'a goge raini tsakanin yan takaran kujeran shugaban kasa 73; mafi yawa a tarihin siyasar Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel