Cikin kwanaki 2 an kashe Mutane 21 a Birnin Gwari - Shehu Sani

Cikin kwanaki 2 an kashe Mutane 21 a Birnin Gwari - Shehu Sani

Wakilin shiyyar Kaduna ta Tsakiya a zauren majalisar dattawan Najeriya, Sanata Shehu Sani, a jiya Lahadi, ya yi karin haske dangane da wani mummunan ta'addanci da ya auku cikin yankin garin Birnin Gwari da ke Kudancin jihar Kaduna.

A jiya Lahadi, Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa, kimanin rayuka 21 na wasu Mutanen karkara sun salwanta a hannun 'yan ta'adda cikin garin Birnin Gwari da ke jihar Kaduna kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Sanata Shehu ya ce wannan mummunar ta'ada ta salwantar rayukan mutane fiye da ashirin ta auku ne cikin kwanaki biyu kacal na Alhamis da Juma'a a makon da ya gabata.

Shehu Sani

Shehu Sani
Source: Twitter

Sanatan ya bayyana hakan ne yayin ganawar sa da manema labarai cikin birnin Minna na jihar Kwara yayin da ya ke kan hanyar sa ta dawowa garin Kaduna bayan ya kammala taron sa na yakin neman zabe.

Shehu ya bayyana damuwar sa kwarai da aniyya dangane da yadda ta'addanci ke ci gaba da salwantar rayukan Mutane a kulli yaumin cikin garin Birnin Gwari, wasu yankunan jihar Neja da kuma jihar Zamfara.

KARANTA KUMA: Sarkin Kano ya yi kira kan tabbatar da zaman lafiya yayin zaben 2019

Ya sake jaddada damuwar sa dangane da yadda ba bu wata hukumar tsaro ta jami'an 'yan sanda ko kuma rundunar dakarun sojin kasa da ta bayar da shaida ta tabbacin ire-iren wannan munanan rahoto da ke ci ga da aukuwa kusan kowace rana.

Sai dai hukumar 'yan sandan jihar da sanadin Kakakin ta, DSP Yakubu Sabo, ta musanta ikirarin Sanata Shehu da ta misalta shi a matsayin shaci fadi tare da cewar ba bu yadda makamancin wannan lamari zai auku ba tare da wata hukuma ta samu masaniyar sa ba.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel