NJC za ta dawo zama yau kan Onnogen da Muhammed

NJC za ta dawo zama yau kan Onnogen da Muhammed

- Majalisar alkalai ta kasaza ta dawo zama a yau domin yanke hukunci akan makomar Shugaban alkalan Najeriya, Walter Onnoghen da mukaddashin Shugaban alkalan kasar, Tanko Muhammed

- Majalisar alkalan a ranar 29 ga watan Janairu ta dage ganawarta zuwa ranar 11 ga watan Fabrairu bayan ta umurci Onnoghen da Muammed da su amsa korafe-korafe da aka yi akansu

- Dukkaninsu su biyun sun bayar da amsoshin tambayoyo amma dai ba a fallasa su ba tukuna

Majalisar alkalai ta kasa (NJC) za ta dawo zama a yau domin yanke hukunci akan makomar Shugaban alkalan Najeriya (CJN) da ke fuskantar shari’a, Walter Onnoghen da mukaddashin Shugaban alkalan kasar, CJN Tanko Muhammed.

Majalisar alkalan a ranar 29 ga watan Janairu ta dage ganawarta zuwa ranar 11 ga watan Fabrairu bayan ta umurci Onnoghen da Muammed da su amsa korafe-korafe da aka yi akansu.

NJC za ta dawo zama yau kan Onnogen da Muhammed

NJC za ta dawo zama yau kan Onnogen da Muhammed
Source: UGC

An tattaro cewa Onnoghen yayi martani ga wani korafi da Zikhirillahi Ibrahim na cibiyar kare akin dan Adam da ilimin jama’a, yayinda an ka tattaro ewa Justis Mohammed ya mayar da martani ga korafe-korafe biyu da cibiyar sari’a da zaman lafiya da kuma lauyan Lagas, Olisa Agbakoba (SAN).

KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa muka yi watsi da Buhari muka kama Atiku – Kungiyar masu ruwa da tsaki a Arewa

Ba a fallasa wa duniya amsosin tambayoyin wanda aka ce anyi su tuna a ranar Talata 5 ga watan Fabrairu ba, amma Justis Onnogen a jawabinsa ga CCB yayi bayanin cewa ya manta bai kaddamar da wasu asusun banki da ke da nasaba dashi ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel