Bani da wata manufa akan Kiristoci – El-Rufai

Bani da wata manufa akan Kiristoci – El-Rufai

- Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Ruai ya ba Kiristoci da ke jihar cewa bashi da wata manufa akansu

- El-Rufai yace hukuncin da ake dauka a karkashin gwamnatinsabata a nasaba da addini ko kabilanci

- Gwamnan yayi bayanin cewa ya zabi mataimakiyarsa a zabe mai zuwa, Dr.Hadiza Balarabe, ne saboda kokarinta ba wai don addini ba

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Ruai ya ba Kiristoci da ke jihar cewa bashi da wata manufa akansu.

Da yake Magana a yayinda wata ganawa da kungiyar Fastoci karkashin inuwar Pastors United For Change Association in Kaduna, El-Rufai yace hukuncin da ake dauka a karkashin gwamnatinsabata a nasaba da addini ko kabilanci.

Bani da wata manufa akan Kiristoci – El-Rufai

Bani da wata manufa akan Kiristoci – El-Rufai
Source: Depositphotos

Gwamnan yayi bayanin cewa ya zabi mataimakiyarsa a zabe mai zuwa, Dr.Hadiza Balarabe, wacce ta fito da karamar hukumar Sanga da ke kudancin Kaduna ne saboda kokarinta ba wai don addini ba.

Gwamnan yace yana aiki tare da mutanen da ke kewaye dashi bisa la’akari da kwarewarsu domin samun sakamako mai kyau ba wai don al’ada ko addini ba sannan yayi kira ga mazauna yankin da su hada kai don ci gaban jihar.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa muka yi watsi da Buhari muka kama Atiku – Kungiyar masu ruwa da tsaki a Arewa

Gwamnan yace yana da yakinin cewa abokiyar takararsa za ta tafiyar da harkokin jihar da kyau sannan za ta yi adalci ga kowa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel