PDP za su saki wasu bidiyoyin bogi domin kashewa Buhari kasuwa - Keyamo

PDP za su saki wasu bidiyoyin bogi domin kashewa Buhari kasuwa - Keyamo

- Kwamitin yakin zaben APC tace PDP na shiryawa Buhari sharri

- Festus Keyamo yayi wannan bayani a wani jawabi da ya fitar jiya

- Kakakin kwamitin yace na kusa da Atiku na neman bata Buhari

PDP za su saki wasu bidiyoyin bogi domin kashewa Buhari kasuwa - Keyamo

Festus Keyamo yace PDP na kitsa labaran karya game da lafiyar Buhari
Source: UGC

Mun ji labari cewa babban kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari na APC sun bayyana cewa jam’iyyar PDP mai adawa na kokarin kitsa sharri game da shugaban kaar mai neman tazarce a zaben da za ayi.

Kakakin kwamitin nay akin tazarcen shugaba Buhari watau Festus Keyamo sho ya bayyana cewa PDP na kokarin kirkirar wasu bidiyoyi na karya domin nunawa Duniya cewa Buhari bai da lafiyar da zai iya cigaba da mulki a Najeriya.

KU KARANTA: Ma’aikatan zabe za su yi rantsuwar yin gaskiya da gaskiya yau

Barista Keyamo a jawabin da ya fitar a karshen makon da ya gabata, yace kwamitin yakin babban ‘dan takarar hamayya watau Atiku Abubakar ne da mutanen sa su ka kitsa wadannan bidiyoyi na karya domin yi wa shugaba Buhari sharri.

Tuni dai har an soma sakin irin wadannan bidiyoyi da sakonni a yanar gizo inda a wani sakon na kwanan nan aka ji wata da sunan Likitar Buhari tana gargadin ‘yan Najeriya cewa shugaban kasar na su bai da isasshen lafiya da zai iya mulki.

Babban Lauya Keyamo yake cewa Atiku Abubakar da mutanen na sa, su na ganin cewa yin wannan zai sa mutane su gujewa sake zaben Buhari domin ya sha kasa a zaben da za ayi a mako mai zuwa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel