2019: Barayin Najeriya sun shirya sayen kuri’ar Talakawa – Buhari

2019: Barayin Najeriya sun shirya sayen kuri’ar Talakawa – Buhari

Mun ji labari cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi magana game da zaben da ake shirya fuskanta a Najeriya inda ya tabbatar da bakin sa cewa zaben da fuskantar babban kalubale a halin yanzu.

2019: Barayin Najeriya sun shirya sayen kuri’ar Talakawa – Buhari

Shugaba Buhari yace ana yunkurin amfani da kudi zaben 2019
Source: Twitter

Shugaba Muhammadu Buhari yace satar kudin al’umma da rashin gaskiya a Najeriya ne ya sabbaba dar-dar din da ake ciki a game da zaben kasar. Shugaba Buhari ya bayyana wannan ne a wani rubutu da yayi kwanan nan.

A wannan rubutu da aka yi a cikin harshen turanci mai suna Corruption threatens Nigeria and election, shugaban kasar yace yana kokari wajen yaki da sata da kuma kawo karshen rashin tsaro da inganta tattalin arzikin Najeriya.

KU KARANTA: Rikice ya barke a Jam’iyyar SDP da tayi wa Buhari mubaya’a

Sai dai shugaba Muhammadu Buhari yana ganin cewa babu abin da yake ba shi wahala irin yaki da satar dukiyar kasa, wanda yake ganin hakan yana da illa ga zaben da za ayi da ma siyasar Najeriya na damukaradiyya gaba daya.

Buhari yake cewa hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tatallin arzikin kasa zagon kasa sun koka da cewa ana shirin amfani da kudin sata wajen ganin an saye kuri’un jama’a a zaben bana wanda saura kusan mako guda a gudanar.

Shugaban na Najeriya yake cewa wadanda su kayi sata daga asusun gwamnati na da niyyar yin amfani da dukiya wajen ganin an yi abin da su ke so a zaben bana yayin da Talakawa ke cikin wani hali na ha-ula’i su kuma ko a jikin su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel