Manjo Janar David Ejoor ya bar Duniya yana da shekaru 87

Manjo Janar David Ejoor ya bar Duniya yana da shekaru 87

- Tsohon babban Sojan Najeriya Janar David Ejoor ya rasu

- Janar David Ejoor ya mutu yana da shekaru 87 a Duniya

- Ejoor ya rike Gwamna da wasu mukamai a cikin gidan Soja

Manjo Janar David Ejoor ya bar Duniya yana da shekaru 87

Wani Tsohon Shugaban hafsun sojan Najeriya ya cika
Source: Depositphotos

Mun samu labari cewa rasuwar tsohon shugaban hafsun sojan Najeriya, David Ejoor ya rasu. Ejoor ya rike wannan babban mukami ne tsakanin 1971 zuwa 1975 a lokacin mulkin shugaban sojan Najeriya Janar Yakubu D. Gowon.

David Ejoor mutumin kasar Delta ne na kabilar Urhobo wanda ya rike matsayin gwamna na kasar karshe da aka kirkira daga 1966 zuwa 1967. Gwamatin jihar Delta ta sanar da mutuwar wannan Bawan Allah jiya a cikin takaici.

KU KARANTA: Dattawan Arewa sun bi layin Shugaba Buhari a zaben 2019

Janar David Ejoor ya kuma zama kwamadan Makarantar Sojoji na Najeriya watau NDA ta Kaduna daga 1969 zuwa 1971. Bayan nan ne Manjo Janar Ejoor ya zama hafsun sojojin kasa na tsawon shekaru 4 kafin yayi ritaya da aiki a gidan soja.

Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta yayi jimamin rasuwar wannan babban Sojan kasar da aka yi a jiya Lahadi. Gwamnan yayi wannan bayani ne ta bakin babban Sakataren yada labarai na jihar Delta, Charles Aniagwu, a garin Asaba.

Gwamnatin jihar Delta ta aikawa dangin mamacin da kuma daukacin kabilar Urhobo da mutanen yankin Ovwor-Olomu na cikin karamar hukumar Ughelli a Delta ta’aziyyar wannan rashi da su kayi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel