Jami’an INEC za su dauki alkawarin yin adalci a zaben 2019 – INEC

Jami’an INEC za su dauki alkawarin yin adalci a zaben 2019 – INEC

- Jami’an Hukumar INEC za su dauki rantsuwar aiki a makon nan

- Saura kusan mako guda a gudanar da babban zaben 2019 a kasar

- Za a fadakar da Jami’an Hukumar game da yin adalci da gaskiya

Jami’an INEC za su dauki alkawarin yin adalci a zaben 2019 – INEC

Ma'aikatan INEC sun fara shiryawa zaben da za ayi
Source: Depositphotos

Kwanan nan ne labari ya zo mana cewa jami’an zabe na kasa na hukumar INEC su na cigaba da kara kaimi game da zaben bana. A jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya, yau ne ma’aikata za su yi wata rantsuwar aiki.

Hukumar zabe na kasa mai zaman kan-ta, ta bayyana cewa, a yau Litinin 11 ga Watan nan ne manyan ma’aikatan hukumar INEC za su yi rantsuwar yin aikin su kamar yadda dokar aiki da kuma tsarin mulkin kasar ya tanada.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya gaza daga hannun wani 'Dan takara a jihar Zamfara

Farfesa Francis Chukwuemeka Ezeonu, wanda shi ne babban kwamishinan zabe na yankin Imo, ya bayyana cewa a yau ne ma’aikatan sa za su yi rantsuwa tare da kuma sanin aikin da za su yi a zaben da za ayi kwanan nan.

Chukwuemeka Ezeonu ya kuma kara da cewa jami’an zaben za su abin da doka ta tanada ga duk wani jami’in zaben da ya ci amanar aikin da ke kan sa. Babban Jami’in yayi bayani ne ta hannun Mai magana da yawun INEC.

Jami’ar da ke da nauyin yada labarai a yankin, mai suna Emmanuela Okpara, tace dole ma’aikata su yi aiki ba tare da nuna son kai da banbancin ba. Wannan dai shi ne dalilin tara ma’aikatan su rantse da yin adalci a zaben kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel