Dalilin da ya sa mutanen jihar Legas ba za su zabi Atiku ba – Tinubu

Dalilin da ya sa mutanen jihar Legas ba za su zabi Atiku ba – Tinubu

- A ranar Asabar ne shugaba Buhari da tawagar yakin neman zaben jam’iyyar APC su ka ziyarci jihar Legas

- Da ya ke gabatar da jawabi a wurin taron kamfen din, jagoran jam’iyyar APC na kasa, Bola Tiniubu ya ce jihar Legas ta sha wahala a mulkin PDP

- Kazalika, Adams Oshiomhole, shugaban jam’iyyar APC na kasa, y ace zaben da za a yi zai kasance tsakanin talaka ne da ma su kudi

Jagoran jam’iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, ya shaida wa jama’a a jihar Legas cewar dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, bai cancanci kuri’ar su ba saboda bai damu da bukatar su ba a lokacin da ya ke mataimakin shugaban kasa.

Da ya ke Magana a wurin taron yakin neman zaben shugaban kasa da aka yi ranar Asabar a jihar Legas, Tinubu, ya ce tsohon shugaban kasa Obasanjo da mataimakin sa Atiku sun wahalar da jihar Legas tare da saka ta cikin mawuyacin hali, kuma yanzu ne lokacin da jama’ar Legas za su dauki fansar abinda aka yi ma su.

Dalilin da ya sa mutanen jihar Legas ba za su zabi Atiku ba – Tinubu

Atiku da Tinubu
Source: UGC

A nasa bangaren, shugaba Buhari ya shaidawa miliyoyin jama’ar da su ka halarci taron kamfen din sa a filin wasa na Teslim Balogun da ke Surulere a Lagos, cewar ‘yan Najeriya na bin sa bashin hukunta duk wani mutum da ya saka su a wahala ta hanyar sace kudaden gwamnati.

DUBA WANNAN: Atiku ko Buhari: Zai yi wuya a iya hasashen waye zai yi nasara – Ekweremadu

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi osinbajo, ya ce idan aka sake zaben su za su mayar da hankali wajen kirkirar aiyuka, samar da wutar lantar ki da ababen more rayuwa.

Shi kuwa Oshiomhole, shugaban jam’iyyar APC na kasa, gargadi ya yi wa jama’a a kan hatsarin da ke tattare da sake zaben jam’iyyar PDP domin dawowa kan karagar mulkin kasar nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel