So-ko-sakarci: Wani matashi yayi alkawarin kashe kan sa idan Buhari ya fadi zaben da za'a yi

So-ko-sakarci: Wani matashi yayi alkawarin kashe kan sa idan Buhari ya fadi zaben da za'a yi

Wani matashi dake ikirarin zama dan a-mutun shugaban kasar Najeriya kuma dan takarar tazarce a jam'iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC) watau Shugaba Muhammadu Buhari mai suna Adamu Kabir Matazu yayi barazanar kashe kan sa idan Buharin ya fadi zabe.

Matashin wanda ya rubuta sakon na sa a shafin sa na sadar da zumuntar zamani na facebook ya bayyana cewa: "Idan dai har shugaba Buhari ya fadi zaben da za'a gudanar a ranar 16 ga watan Fabreru to zan kashe kaina kafin ranar 29 ga watan Mayu."

So-ko-sakarci: Wani matashi yayi alkawarin kashe kan sa idan Buhari ya fadi zaben da za'a yi

So-ko-sakarci: Wani matashi yayi alkawarin kashe kan sa idan Buhari ya fadi zaben da za'a yi
Source: Facebook

KU KARANTA: Maryam Babban Yaro ta bar tafiyar Buhari ta koma ma Atiku

Ya kara da cewa shi zai kashe kan sa ne domin kuwa ba zai iya jure ganin an rantsar da Atiku ba a matsayin shugaban kasar Najeriya bayan ya kada Buhari.

Tuni dai maganar ta kisan kan nasa da ya wallafa a shafin sa ta ja hankalin al'uma tare da haifar da zazzafar muhawara a tsakanin masoyan bangarorin 'yan siyasar biyu watau Buhari da Atiku.

Wasu dai na ganin bai aikata wani laifi ba kuma tsabar soyayya ce yayin da wasu kuma ke ganin tsabar rashin hankali ne da tunani.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel