Sakon bidiyon Buhari: Za mu cigaba da kare hakkin ku

Sakon bidiyon Buhari: Za mu cigaba da kare hakkin ku

A yammacin yau, Lahadi, ne Femi Adesina, mai taimakawa kakakin shugaban kasa, ya fitar da wani faifan bidiyo da shugaba ya yi Magana da ‘yan Najeriya ta cikin sa.

A cikin faifan bidiyon, shugaba Buhari ya fara da cewa, “ya jama’ar Najeriya, yau fiye da shekaru uku Kenan da ku ka zabe mu domin tafiyar da harkokin gwamnatin kasar mu.

“kun dora mana nauyi mai wahalar gaske amma da goyon bayan ku da sadaukar wa mun samu gagagrumar nasara.

“Daga cikin irin nasarorin da mu ka samu akwai na zahiri da za a iya gani, akwai kuma wadanda har yanzu aiki ake a kan su.

Sakon bidiyon Buhari: Za mu cigaba da kare hakkin ku

Buhari
Source: Depositphotos

“ Ina mai sake neman goyon bayan ku a karo na biyu domin ku sake zabe na a matsayin shugaban kasa domin mu dora a kan nasarorin da mu ka samu da kuma kara nganta kasar mu. Ba zan taba zama mai butulci gare ku ba. Za mu cigaba da aiki domin kare hakkin ku da kuma ganin mun sauke nauyin a ku ka dora ma na.

DUBA WANNAN: Atiku ko Buhari: Zai yi wuya a iya hasashen waye zai yi nasara – Ekweremadu

Kalli faifan bidiyon a kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel