APC-ta-shiga-rudu: Shugaba Buhari ya kasa daga hannun dan takara a jihar Zamfara

APC-ta-shiga-rudu: Shugaba Buhari ya kasa daga hannun dan takara a jihar Zamfara

Gwamnan jihar Zamfara dake a shiyyar Arewa maso yammacin Najeriya kuma shugaban gwamnonin tarayyar Najeriya, Alhaji Abdulaziz Yari da sauran mukarraban sa na jam'iyyar APC sun sha kunya bayan da shugaba Buhari ya ki daga hannun dan takarar gwamna a jihar.

Mun samu cewa dai rikicin 'yan takarar jam'iyyar APC a jihar ta Zamfara ne dai ya hana shugaba Muhammadu Buhari daga hannun dan takarar gwamna a jihar.

APC-ta-shiga-rudu: Shugaba Buhari ya kasa daga hannun dan takara a jihar Zamfara

APC-ta-shiga-rudu: Shugaba Buhari ya kasa daga hannun dan takara a jihar Zamfara
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Shugaba Buhari yayi wa barayin gwamnati Allah-ya-isa

A yayin yakin neman zabensa a Zamfara a ranar Lahadi, Buhari ya ce "duk gardamar da ake idan abu yana wurin shari'a za mu dakata."

Hakan dai ya kara tabbatar da cewa APC a Zamfara na cike da rudani bayan shugaban ya kasa daga hannun 'yan takara.

Kafin jawabin Buhari, gwamnan jihar mai barin gado Abdulaziz Yari Abubakar ya ce ba za su tilasta wa shugaban daga hannun 'yan takara ba kamar sauran jihohi amma ya ce da yardar Allah da 'yan takarar APC za a yi zaben 2019.

A cikin jawabinsa a Zamfara, shugaba Buhari ya ce yana fatan kafin ranar Asabar, hukumar zabe za ta fito ta fadi dan takarar da ta yadda da shi.

Sai dai kuma Buhari ya yi kira ga mutane su fito su zabi wanda suke so, a gaban gwamnan Zamfara da ke gawagwarmayar tabbatar da kwamishinansa na kudi a matsayin gwamna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel