Cikin Hotuna: Shugaba Buhari ya gudanar da yakin zaben sa a jihar Zamfara

Cikin Hotuna: Shugaba Buhari ya gudanar da yakin zaben sa a jihar Zamfara

A yayin da a yau Lahadi dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya gudanar da taron sa na yakin neman zabe a jihar Kano, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gudanar da nasa taron cikin birnin Gusau na jihar Zamfara.

Yayin dirar shugaban kasa Buhari a safiyar yau ta Lahadi, ya gudanar da wani zaman sauraron ra'ayin al'umma domin tattaunawa akan kalubalai na rashin tsaro musamman annobar ta'addancin masu garkuwa da mutane da kuma barayi shanu da suka addabi al'ummar jihar.

Shugaba Buhari yayin dirar sa jihar Zamfara

Shugaba Buhari yayin dirar sa jihar Zamfara
Source: Twitter

Tururuwar al'umma yayin yiwa Shugaba Buhari lale maraba a jihar Zamfara

Tururuwar al'umma yayin yiwa Shugaba Buhari lale maraba a jihar Zamfara
Source: Twitter

Buhari yayin zaman sauraron ra'ayi cikin fadar gwamnatin jihar Zamfara

Buhari yayin zaman sauraron ra'ayi cikin fadar gwamnatin jihar Zamfara
Source: Twitter

Shugaban kasa Buhari yayin tattaunawa akan hanyoyin inganta tsaro a jihar Zamfara, ya kuma jajantawa 'yan uwan wadanda rikicin ta'ddanci ya afkawa ta fuskar salwantar rayuka, muhallai da kuma dukiyoyin su.

KARANTA KUMA: Rayuka 3 sun salwanta yayin yakin zaben Atiku a jihar Kano

Da yake jan hankalin hukumomin tsaro cikin fadar gwamna Abdul aziz Abubakar Yari akan zage dantse da tumke damara wajen sauke nauyin da rataya a wuyan su, ya kuma kirayi Sarakunan gargajiya na jihar da su ribaci rawanin su wajen jibintar al'amurran talakawan su.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel