Rayuka 3 sun salwanta yayin yakin zaben Atiku a jihar Kano

Rayuka 3 sun salwanta yayin yakin zaben Atiku a jihar Kano

Mun samu cewa, kimanin rayukan Mutane uku ne suka salwanta tare da sumewar Mutane fiye da talatin yayin yakin neman zabe na dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, da aka gudanar a yau Lahadi cikin birnin Kano.

Rahotanni kamar yadda shafin jaridar The Nation ta ruwaito sun bayyana cewa, rayukan mutane sun salwanta a sakamakon wani rikici da ya barke tsakanin wasu 'yan adawa daura da filin wasanni na Sani Abacha inda aka gudanar da taron na yakin zabe.

Ko shakka ba bu Atiku da tawagar sa ta jiga-jigan jam'iyyar PDP sun girgiza magoya baya yayin gudanar da taron yakin neman zaben kujerar shugaban kasa da aka gudanar cikin babban birni na Kanon Dabo.

Hoton wani Matashi da ya suma yayin yakin zaben Atiku a jihar Kano

Hoton wani Matashi da ya suma yayin yakin zaben Atiku a jihar Kano
Source: Twitter

KARANTA KUMA: Kamfe: Atiku ya gigita al'ummar jihar Kano

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, dumbin al'umma tamkar ridi sun yi tururuwa a harabar taron ta Sani Abacha yayin kiradadon zuwan Atiku da kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Kwankwaso tsawon sa'o'i da dama.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel