Zaben 2019: Jam’iyyar mu ta ba mu kunya na tsaida Buhari – Jerry Gana

Zaben 2019: Jam’iyyar mu ta ba mu kunya na tsaida Buhari – Jerry Gana

Kungiyar yakin neman zaben Farfesa Jerry Gana watau ProfessorJerry Gana Campaign Group wanda aka fi sani da G19 ta nesanta kan ta daga goyon bayan da jam’iyyar sa ta SDP ta ba shugaban kasa Buhari.

Zaben 2019: Jam’iyyar mu ta ba mu kunya na tsaida Buhari – Jerry Gana

Jerry Gana ya caccaki Jam’iyyar sa a dalilin marawa Buhari baya
Source: Depositphotos

Kwanan nan ne jam’iyyar adawa ta SDP ta bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari shi ne ‘dan takarar ta a zaben shugaban kasar da za ayi kwanan. Jerry Gana wanda yana cikin masu neman takara a jam’iyyar yayi tir da hakan.

Jerry Gana yake cewa marawa ‘dan takarar APC mai mulki watau shugaba Muhammadu Buhari da jam’iyyar sa tayi abin kunya ne kuma ya nuna yunwar jam’iyyar a fili. Gana ya kuma ce SDP ta ci amanar goyon bayan Mabiyan ta.

Farfesa Gana ya fitar da jawabi ne inda ya nuna cewa ba ya tare da wannan mataki da jam’iyyar sa ta dauka na tsaida Buhari a matsayin ‘dan takarar ta a zaben bana. Farfesan yace wani jigo a cikin jam’iyyar ne duk ya kitsa wannan aiki.

KU KARANTA: An kusa hallaka wani ‘Dan takara a Kudancin Najeriya

Tsohon ministan kasar ya daura laifin wannan mubaya’a da jam’iyyar hamayyar tayi wa shugaban kasa Buhari na APC ne a kan Shehu Gabam wanda shi ne babban Sakataren jam’iyyar. Wani Dr. Ike Neliaku yayi wannan jawabi a Abuja.

Ike Neliake wanda yake tare da Gana yace wannan abu da jam’iyyar tayi yana iya kawo mata cikas a zaben 2019, inda yace hakan na iya jawowa sauran ‘yan takarar ta bakin jini. Yanzu dai saura mako guda a gudanar da zabe a Najeriya.

A jawabin na Gana, ya zargi bangaren jam’iyyar da ke tare da Donald Duke da jefa jam’iyyar cikin wannan rikici. Sai dai shi ma Donald Duke ya nuna cewa ba ya goyon bayan Buhari a zaben da za ayi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel