Da duminsa: An yi awa 2 ana bata kashi tsakanin Boko Haram da sojoji a Madagali

Da duminsa: An yi awa 2 ana bata kashi tsakanin Boko Haram da sojoji a Madagali

Rahotannin da Legit.ng Hausa ta samu, na nuna cewa sojojin Nigeria sun yi ba-ta-kashi da mayakan Boko Haram a garin Madagali, jihar Adamawa, indas suka samu nasarar kashe daya daga cikin 'yan ta'addan. Yayin da mayakan na Boko Haram suka kashe mai garin kauyen Gubla.

Mazauna yankin sun bada rahoton cewa mayakan Boko Haram dauke da muggan makamai sun mamaye garin da misalin akrfe 5 na yamma a jiya Asabar, inda suka fara musayar wuya da jami'an soji, har na tsawon awanni biyu.

Wani da harin ya faru gaban idonsa ya ce karar harbe harben bindigogi ya mamaye sararin samaniya, inda ya tilasta fararen hula neman mafaka a tsaunukan da ke kusa da garin, har sai zuwa safiyar ranar Lahadi, bayan samun labarin cewa sojojin sun ci galabar 'yan ta'addan.

KARANTA WANNAN: Zargin sama da fadi da N6.4m: Babachir Lawal zai gurfana gaban kotu ranar Talata

Da duminsa: An yi bata kashi tsakanin Boko Haram da soji a Madagali

Da duminsa: An yi bata kashi tsakanin Boko Haram da soji a Madagali
Source: Twitter

A wani labarin kuma, mayakan Boko Haram da suka kai hari a kauyen Gubla da ke nesa kadan da Madagali, sun kashe mai garin garin, Ali Kirim, kamar yadda wata majiya daga iyalan mai garin ta sanar.

Tsohon shugaban karamar hukumar Madagali, Yusuf Muhammad, ya tabbatar da kashe mai garin kauyen, yana mai cewa 'yan ta'addar ne suka harbesa a kan hanyarsa ta komawa kauye daga cikin garin Madagali.

Sai dai har zuwa kammala rubuta wannan labarin, duk wani yunkuri na tuntubar jami'an soji na Yola ya ci tura, a yayin da mai magana da yawun rundunar 'yan sanda na jihar, Othman Abubakar ya ce yana wajen halartar wani taron bita a Abuja.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel