Zargin sama da fadi da N6.4m: Babachir Lawal zai gurfana gaban kotu ranar Talata

Zargin sama da fadi da N6.4m: Babachir Lawal zai gurfana gaban kotu ranar Talata

- Wata babbar kotun gwamnatin tarayya ta sanya ranar 12 ga watan Fabreru a matsayin ranar da za a gurfanar mata da Babbachir Lawal

- Hukumar EFCC ta maka Lawal ne gaban mai shari'a Jude Okeke, akan zarginsa da aikata laifuka 10 tare da Hamidu David Lawal, Suleiman Abubakar da wasu kamfanoni 2

- A cikin watan Oktoba 2017, shugaba Buhari ya kori Lawal biyo bayan wani rahoton bincike da kwamitin Yemi Osinbajo ya gabatar kan wannan zargi

Wata babbar kotun gwamnatin tarayya da ke da zama a Maitama, ta sanya ranar 12 ga watan Fabreru a matsayin ranar da za a gurfanar mata da tsohon sakataren gwamnatin tarayya (SGF) Babbachir Lawal tare da wasu mutane biyar.

Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa da yiwa dukiyar kasa zagon kasa, EFCC ta maka Lawal ne gaban mai shari'a Jude Okeke, akan zarginsa da aikata laifuka 10 da suka shafi sama da fadi da kudaden kasa tare da Hamidu David Lawal, Suleiman Abubakar da wasu kamfanoni 2, Rholavision Engineering Ltd da Josmon Technologies Ltd.

KARANTA WANNAN: Kar ku biyewa zantukan 'yan adawa, ku zabeni a Maris - El-Rufai ya roki Kirista

Zargin sama da fadi da N6.4m: Babachir Lawal zai gurfana gaban kotu ranar Talata

Zargin sama da fadi da N6.4m: Babachir Lawal zai gurfana gaban kotu ranar Talata
Source: UGC

A karar da aka shigar a ranar 30 ga watan Janairu, wacce Offem Uket ya shigar a madadin hukumar, ana zargin Lawal da hada baki da Hamidu, darakta a kamfanin Rholavision da Abubakar, ma'aikata a kamfanin, domin mallakar wata kadara, wanda ya sabawa sashe na 26(1)(c) na dokar laifukan cin hanci da rashawa da dangoginsu, ta shekarar 2000, kuma hukuncin laifin na karkashin sashe na 12 na dokar.

Daya daga cikin laifukan da ake tuhumar Hamidu, Abubakar da kamfanin Rholavison shine mallaka kwangila a madadin kamfanin na cire wasu ciyayi da kuma saukaka noman rani da kudin kwangilar ya kai N6.4m daga ofishin sakataren gwamnatin tarayya karkashin shirin bunkasa Arewa maso Gabas na shugaban kasa (PINE).

A cikin watan Oktoba 2017, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kori Lawal biyo bayan wani rahoton bincike da kwamitin shugaban kasar ya gudanar bisa jagorancin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, kan wannan zargi na sama da fadi da ake yiwa Lawal.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel