Kar ku biyewa zantukan 'yan adawa, ku zabeni a Maris - El-Rufai ya roki Kirista

Kar ku biyewa zantukan 'yan adawa, ku zabeni a Maris - El-Rufai ya roki Kirista

- Nasir el-Rufai, gwamnan jihar Kaduna, ya bukaci daukacin malumman Kirista da su goya masa baya a babban zaben 2019 da ke gabatowa

- El-Rufai ya yi kira ga daukacin al'ummar Kirista a jihar da su kauda batun addini tare da mayar da hankali kan irin ayyukan raya kasa da gwamnan ya yi a jihar

- A nashi jawabin, Apostle David Adeniran, shugaban kungiyar PUCA, ya ce ya na da yakinin cewa malumman Kirista za su koma gida da sabon tunani kan gwamnan

Nasir el-Rufai, gwamnan jihar Kaduna, ya bukaci daukacin malumman Kirista da su goya masa baya a babban zaben 2019 da ke gabatowa.

A wani taron da ya gudanar da malaman Kiristan, karkashin kungiyar hadin kan malaman Kirista (PUCA), wanda ya gudana a Kaduna a ranar Asabar, El-Rufai ya yi kira ga daukacin al'ummar Kirista a jihar da su kauda batun addini tare da mayar da hankali kan irin ayyukan raya kasa da gwamnan ya yi a jihar.

El-Rufaiu na neman tazarcen kujerar gwamnan jihar, inda ya zabi Dr. Hadiza Balarabe, wacce Musulma ce a matsayin abokiyar takararsa.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: Gobara ta lakume kayan zabe a ofishin INEC na jihar Filato, duba hotuna

Gwamna El-Rufai tare da Dr. Hadiza

Gwamna El-Rufai tare da Dr. Hadiza
Source: UGC

Wannan rokon nasa ya biyo bayan wata daya da wani jawabi da ya yi, inda ya bayyana cewa ko da ace Fafaroma ne ya ke a matsayin abokin takararsa, kashi 67 na al'ummar Kirista a jihar Kaduna ba za su zabe shi ba.

Sai dai, a yayin taron jin ra'ayoyin jama'a a ranar Asabar, ya ce: "A rayuwata, ban taba aiki da mutane ta hanyar la'akari da addininsu ko kabilarsu ba. Kar ku duba abubuwan da mutane ke fada, amma abubuwan da na aikata na raya kasa a baya.

"Ku je ku duba irin ayyukan raya kasa da na yi. Dan gane da abokiyar takarata kuwa, munyi hakan ne domin baiwa mata kwarin guiwa na shiga harkokin siyasa. Hakika mace ce wacce ta cancanta. A jihar Kaduna ne kadai ake da 'yan takarar gwamna mace da namiji a Arewacin Nigeria."

A nashi jawabin, Apostle David Adeniran, shugaban kungiyar PUCA, ya ce: "Ina da yakinin cewa da yawa daga cikinmu za su koma gida da sabon tunani na cewar kyawawan abubuwa na faruwa a Kaduna. Wannan ita ce sabuwar jihar Kaduna."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel